Mai taimaka wa shugaban Æ™asa a kan kafafen yada labarai, Abdulaziz Abdulaziz, ya bayyana cewa ko baya cikin gwamnatin Bola Tinubu, ba zai shiga zanga-zangar da ake kokarin yi a watan Agusta ba.Â
Abdulaziz, ya bayyana haka ne a shafinsa Facebook a safiyar yau Laraba, inda ya mayarwa da waÉ—anda suke nemo tsofaffin rubuce-rubucensa na baya da ya yi na shiga zanga-zanga.
- Babu Tabbacin Ko Ederson Zai Ci Gaba Da Zama A Manchester City – Guadiola
- Sojoji Sun Sake Ceto Daya Daga Cikin ‘Yan Matan Chibok
Ya ce “Masu tone-tonen tsoffin rubutuna ba sai kun ba wa kanku wahala ba!
“Na shiga zanga-zanga guda biyu a baya. Na shiga ta cire tallafin man fetur a 2012 a Kano na kuma shiga ta ‘Bring Back Our Girls’ a Abuja a 2014. Duka wadancan zanga-zanga suna da tsari da shugabanci da kuma sanin inda aka dosa.
Yawanci kafin fita zanga-zanga ana fitar da tsarin yadda za ta gudana da kuma irin abin da masu zanga-zangar suke buƙata, hakan ya sa Abdulaziz ya ce wannan ba ta da tsarin da ya kamata a shiga.
“Amma a 2019 ban shiga zanga-zangar ENDSARS ba saboda (kamar yadda na faÉ—a a wancan lokacin) ba ta da tsarin shugabanci da takamammiyar manufa (idan ban da Æ™oÆ™arin tunzura mutane da yi wa gwamnati tawaye wadda kuma kan kai ga jefa Æ™asa cikin ruÉ—ani). Na É—auki wannan matsayar ne duk da bani da alaÆ™a ta kusa ko ta nesa da gwamnatin Buhari.
“Zanga-zangar da ake shirin yi ta August b ata da bambanci da ta Endsars don haka ko da ba na cikin gwamnati ba zan taÉ“a goyon bayanta ba.”
Batun zanga-zanga dai shi ne abin da ake yawan tattaunawa a shafukan sada zumunta a Nijeriya a ‘yan kwanakin nan, sai dai har yanzu ba a san jagororin zanga-zangar ba.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ta bakin ministan yaɗa labarai, ya roƙi matasan da suke shirya zanga-zangar da cewa su sake bashi lokaci domin ya saisaita lamuran ƙasar nan.
Sai dai tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, wanda kuma tsohon É—an takarar shugaban Æ™asa ne a jam’iyyar adawa ta PDP, ya soki gwamnatin tarayya, inda ya ce waÉ—anda suke cewa ka da a yi zanga-zangar su ne waÉ—anda suka jagoranci wadda aka yi a baya.