• English
  • Business News
Monday, November 3, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Me Ya Sa Aka Yi Taron Sulhu Tsakanin Mabambantan Bangarori Na Palasdinu a Beijing?

by Sulaiman and CGTN Hausa
1 year ago
Beijing

Bangarori 14 na Palasdinu sun kulla yarjejeniyar dinke baraka da wanzar da hadin kan al’ummar Palasdinu a jiya Talata a Beijing, bayan sun gudanar da shawarwarin neman sulhu a tsakaninsu daga Lahadi zuwa Talatar nan. Sanarwar ta tabbatar da cewa, kungiyar ’yantar da al’ummar Plasdinawa wato PLO ita kadai take da ikon wakiltar al’ummar kasar, kuma an kai ga matsaya daya kan yadda za a gudanar da harkokin Gaza bayan yaki da kafa gwamnatin sulhuntawar al’umommin kasar na wucin gadi.

Da wuya aka samu ci gaba mai armashi wajen wanzar da zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya, abin da ya baiwa al’ummar Palasdinawa wadanda suke fama da yake-yake makoma mai haske. A madadin sauran bangarorin, shugaban tawagar Fatah Mahmud Alul da shugaban tawagar Hamas Mousa Mohammed Abu Marzook sun yi jawabi, inda suka gode da taimakon da Sin ta dade tana baiwa Palasdinu ba tare da wani sharadi ba, kuma suna jinjinawa matakin da Sin take dauka na nacewa ga adalci kan abubuwan dake shafar mata a duniya.

  • Wang Yi Ya Tattauna Da Ministan Harkokin Wajen Ukraine
  • Za Mu Bankado Masu Yi Wa Nijeriya Zagon Kasa — Majalisa

To, me ya sa bangarori daban-daban na Palasdinu suka sake zabar Beijing domin yin shawarwarin neman sulhu tsakaninsu? Dalili shi ne Sin ba ta da nufin cin moriyarta daga wannan batu, tana tsayawa kan wanzar da zaman lafiya da mutuncin bil Adam. Tun daga watan Augusta, lokacin barkewar rikici a sabon zagaye, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana matsayin da Sin take dauka sau da dama, wato dakatar da bude wuta nan da nan da hana yaduwar rikicin da ma nanata cewa, tsarin kafa kasar Palasdinu da Isra’ila shi ne hanya daya tilo da za a bi wajen warware wannan matsala a duk fannoni, kuma cikin adalci da dorewa.

LABARAI MASU NASABA

Shugaba Xi Ya Mika Sakon Taya Murnar Bude Babban Gidan Tarihi Na Kasar Masar

Ziyarar Shugaba Xi A Koriya Ta Kudu Ta Bude Babin Yaukaka Hadin Gwiwar Yankin Asiya Da Fasifik

Saudiyya da Iran sun kai ga matsaya daya a Beijing, zuwa yanzu bangarorin daban-daban na Palasdinu sun sanya hannu kan yarjejeniya, wadannan ci gaban da aka samu na alamanta cewa, Sin na yin iyakacin kokarin ba da taimako wajen wanzar da zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya da samun bunkasuwa. Sin sahihiyar abokiya ce da kasashen Larabawa ke iya dogaro da ita. Hakan ya sa, abun da Sin take yi ke samun amincewa daga bangarori daban-daban dake bukatar shiga tsakani har su kai ga matsaya daya, wanda da ma an yi hasashen cewa abu ne mara yiwuwa. (Amina Xu)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Shugaba Xi Ya Mika Sakon Taya Murnar Bude Babban Gidan Tarihi Na Kasar Masar
Daga Birnin Sin

Shugaba Xi Ya Mika Sakon Taya Murnar Bude Babban Gidan Tarihi Na Kasar Masar

November 2, 2025
Ziyarar Shugaba Xi A Koriya Ta Kudu Ta Bude Babin Yaukaka Hadin Gwiwar Yankin Asiya Da Fasifik
Daga Birnin Sin

Ziyarar Shugaba Xi A Koriya Ta Kudu Ta Bude Babin Yaukaka Hadin Gwiwar Yankin Asiya Da Fasifik

November 2, 2025
Taron APEC Na 2026 Da Za A Shirya A Kasar Sin Zai Bude Sabon Babin Na Gina Al’ummar Bai Daya Ta Asiya-Pasifik
Daga Birnin Sin

Taron APEC Na 2026 Da Za A Shirya A Kasar Sin Zai Bude Sabon Babin Na Gina Al’ummar Bai Daya Ta Asiya-Pasifik

November 2, 2025
Next Post
Sin Ta Samu Karuwar Mafi Yawan Hatsi A Yanayin Zafi A Cikin Shekaru 9

Sin Ta Samu Karuwar Mafi Yawan Hatsi A Yanayin Zafi A Cikin Shekaru 9

LABARAI MASU NASABA

Kwankwaso Ya Gargaɗi Trump Kan Barazana Ga Nijeriya

Kwankwaso Ya Gargaɗi Trump Kan Barazana Ga Nijeriya

November 2, 2025
Gumi Ya Nemi Nijeriya Ta Katse Hulɗa Da Amurka Idan Trump Bai Janye Barazanar Sa Ba

Gumi Ya Nemi Nijeriya Ta Katse Hulɗa Da Amurka Idan Trump Bai Janye Barazanar Sa Ba

November 2, 2025
Shugaba Xi Ya Mika Sakon Taya Murnar Bude Babban Gidan Tarihi Na Kasar Masar

Shugaba Xi Ya Mika Sakon Taya Murnar Bude Babban Gidan Tarihi Na Kasar Masar

November 2, 2025
Ƙasashen Da Ba Su Yanke Hukuncin Kisa A Duniya Ba

Ƙasashen Da Ba Su Yanke Hukuncin Kisa A Duniya Ba

November 2, 2025
Ziyarar Shugaba Xi A Koriya Ta Kudu Ta Bude Babin Yaukaka Hadin Gwiwar Yankin Asiya Da Fasifik

Ziyarar Shugaba Xi A Koriya Ta Kudu Ta Bude Babin Yaukaka Hadin Gwiwar Yankin Asiya Da Fasifik

November 2, 2025
Yadda Za Ku Hada Fab Biskit

Yadda Za Ku Hada Fab Biskit

November 2, 2025
Kano Pillars Ta Koma Matsayi Na 20 Bayan Shan Kashi A Hannun Enyimba

Kano Pillars Ta Koma Matsayi Na 20 Bayan Shan Kashi A Hannun Enyimba

November 2, 2025
Wolves Ta Kori Da Kocinta Vitor Pereira Sakamakon Rashin Nasara

Wolves Ta Kori Da Kocinta Vitor Pereira Sakamakon Rashin Nasara

November 2, 2025
Musabbabin Hana Sule Lamido Fom Ɗin Takarar Shugabancin PDP

2027: Yadda Gwamnoni Suka Yi Fatali Da Mataimakansu Wajen Zaɓo Waɗanda Za Su Gaje Su

November 2, 2025
Gidauniyar IRM Da KADCHMA Ta Ƙaddamar Da Inshorar Lafiya Kyauta Ga Mutane 200 A Kaduna

Gidauniyar IRM Da KADCHMA Ta Ƙaddamar Da Inshorar Lafiya Kyauta Ga Mutane 200 A Kaduna

November 2, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.