Gwamnatin jihar Bauchi ta ce, babu batun wata zanga-zangar tsadar rayuwa da za a yi balle zancen rufe asibitoci a fadin jihar.
Sakataren gwamnatin jihar Bauchi, Barista Muhammad Ibrahim Kashim shi ne ya sanar da matsayar gwamnati a yayin da ke ganawa da ‘yan jarida a ranar Laraba.
- Tinubu Ya Gana Da Gwamnonin APC Kan Zanga-zangar Matsin Rayuwa
- Gwaman Bauchi Ya Karya Farashin Taki Zuwa ₦20,000
Idan za a tuna wani jami’in gwamnatin jihar a ranar Talatar da ta gabata ya shelanta cewa su na da wani bayanin da ke cewa akwai shirin kai hari ga asibitoci a ranar gudanar da zanga-zanga kan matsin rayuwa da ake ciki, don haka gwamnatin ta dauki matakin cewa za ta kulle dukkanin kananan asibitoci (PHCs) da suke fadin jihar a ranar zanga-zangar.
Sai dai a martaninsa, sakataren gwamnatin, ya ce wannan jami’in ya yi gaban kansa wajen sanar da batun rufe asibitoci kuma za a hukunta shi daidai da abun da ya yi.
Kan hakan, Ibrahim Kashim ya gargadi duk wani ko wasu da ke shirin gudanar da zanga-zangar matsin rayuwa da cewa ya je wata garin ba dai Bauchi ba, don haka ba batun zanga-zanga a jihar.
Ya ce: “Na tabbatar ku na da rahotonnin da ke zagawa cikin jihar nan da ma kasa na cewa gwamnatin jihar Bauchi ta ba da dama a rufe asibitocinta a cikin jihar da kananan hukumomi don saboda zanga-zangar da ake neman yi.” In ji shi.