A halin yanzu dai shugaban ƙasa Bola Tinubu, yana ganawa da gwamnonin da jam’iyyar APC a karkashin inuwar na ƙungiyar a fadar shugaban kasa da ke birnin Abuja.
Duk da cewa ba a bayyana dalilin taron ga manema labarai ba wanda suke gudanar da shi yau Alhamis, a fadar gwamnati amma ana kyautata zaton yana da nasaba da shirin zanga-zangar yunwa da aka shirya gudanarwa a ranar 1 ga watan Agusta, 2024.
- Ba Mu San Dalilin Da ‘Yan Nijeriya Ke Son Yin Zanga-zanga Ba — Gwamnonin APC
- Mangal Ya Dauki Nauyin Yi Wa Masu Ciwon Mafitsara 80 Aiki A KatsinaÂ
Shugaban kungiyar gwamnonin kuma gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodimma ne, ya jagoranci tawagar gwamnonin zuwa fadar shugaban kasa tare da shugaban kungiyar gwamnonin Nijeriya (NGF), kuma Gwamna jihar Kwara, AbdulRazaq AbdulRahman.
Haka kuma an ga mataimakin gwamnan jihar Edo, Philip Shuaibu, da Gwamnan jihar Benue, Hycinth Alia da takwarorinsa Uba Sani na jihar Kaduna da na jihar Ebonyi, Francis Nwifuru, da dai sauransu duk a fadar shugaban ƙasa.