Kasashen Amurka da Birtaniya da kuma Kanada sun gargadi ‘yan kasarsu mazauna Nijeriya kan yiwuwar samun tashe-tashen hankula a yayin zanga-zangar da aka shirya yi a fadin kasar.
Gargadin ya biyo bayan fargabar da ake yi kan yiwuwar samun tashin hankali yayin gudanar da zanga-zangar da ake shirin yi a fadin kasar na nuna rashin amincewa da tsadar rayuwa da tabarbarewar tattalin arziki wacce aka shirya farawa daga ranar 1 ga watan Agustan 2024.
- Zanga-zanga: Za Mu Yi Amfani Da Dandalin Eagle Square Ko Da Izini Ko Babu A Abuja
- Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Naɗa Sabon Kwamitin Gudanarwa Na Ƙungiyar Kano Pillars FC
A cikin shawarwarin tafiye-tafiye da zirga-zirga daban-daban, kasashen uku sun gargadi ‘yan kasarsu da su guji wuraren da za a iya samun arangama tsakanin hukumomin tsaro da masu zanga-zangar.
A nata shawarar, Ofishin Jakadancin Amurka a Abuja, ya bukaci Amurkawa da su guji tarukan, inda ta shawarce su da su guji cunkoson jama’a da zanga-zangar sannan kuma su kasance cikin shirin samun sabbin rahotonni daga kafafen sadarwa na cikin gida.
Wadannan shawarwarin sun nuna tsananin damuwa kan zanga-zangar da aka shirya yi a fadin kasar da kuma tasirinsu kan tsaro a Nijeriya.