Hukumar Sadarwa ta ƙasa (NCC) ta ba da umarni ga kamfanonin sadarwa da su gaggauta sake haɗa layukan wayar da aka katse saboda matsalar tabbatar da NIN-SIM. Daraktan yaɗa labarai da hulɗa da Jama’a na NCC, Reuben Muoka, ne ya fitar da wannan sanarwa a yau Litinin.
Wannan matakin ya biyo bayan mummunan fushi da bacin rai da masu amfani da layukan suka yi, musamman waɗanda suka mamaye ofisoshin MTN a faɗin Nijeriya yau 29 ga Yuli, bayan da aka katse layukansu bisa zargin gazawar hade Lambobin Shaida NIN da lambobin wayar su.
- Sin Da Amurka Sun Amince Da Ci Gaba Da Tuntubar Juna A Dukkanin Matakai
- Amfanin Almiski Da Sabulunsa (2)
MTN ta katse layuka da dama a jiya Lahadi, domin bin umarnin da NCC ta bayar na datse layukan SIM da ba a haɗa da NIN ba.
Tun da farko, NCC ta sanya wa’adin ranar 31 ga Yuli, 2024, don kammala haɗewar NIN-SIM, bayan da aka daga wa’adin daga ranar 15 ga Afrilu, 2024. Hukumar ta yi gargaɗi cewa masu amfani da layuka miliyan 45 za su iya fuskantar matsala idan ba su bi ka’idojin hadewar ba.
Saboda ci gaba da samun matsaloli da koke-koken masu amfani da layuka, umarnin da NCC ta bayar na baya-bayan nan ya nufi rage wannan matsalar ta hanyar tabbatar da cewa an sake kunna layukan da abin ya shafa nan take. Wannan matakin ana sa ran zai kawo sauki ga miliyoyin masu amfani da suka samu kansu a tsaka mai wuya, tare da kyautata tsarin tabbatar da rijistar NIN-SIM a nan gaba.