MTN ta sanar da rufe dukkan ofisoshinta a faɗin Nijeriya na tsawon awanni 24, farawa daga 30 ga Yuli, 2024. Wannan matakin ya biyo bayan hare-haren lalata kayayyakin cibiyar sadarwar da wasu suka yi saboda katse layukansu da MTN ta yi sakamakon rashin haɗa NIN-SIM.
A cikin wata sanarwar da aka fitar a X, MTN ta shawarci abokan cinikinta da su yi amfani da tashoshin tallafi na intanet domin samun taimakon da suke nema yayin rufe ofisoshin, tare da bayar da cikakken bayani kan yadda za a buɗe layukan waya ta intanet.
- NCC Ta Umarci Kamfanonin Sadarwa Su Gaggauta Sake Haɗa Layukan Wayar Da Aka Katse Saboda NIN-SIM
- Hada Layuka Da NIN: MTN Ta Kulle Layuka Miliyan 4.2 A Nijeriya
Wannan matakin na da nasaba da wata zanga-zangar da aka yi a yankin Festac Town a Lagos, inda wasu masu layi suka lalata katangar wani ofishin MTN saboda katse layukan wayarsu. MTN ta tabbatar wa abokan hulɗar ta cewa za a ci gaba da gudanar da ayyuka kamar yadda aka saba bayan rufewar ta awanni 24, tare da jaddada aniyar warware matsalolin da suka shafi haɗa layin NIN-SIM.
Jaridar LEADERSHIP ta ruwaito cewa kamfanin ya ɗauki wannan matakin ne domin tabbatar da tsaron ma’aikatansa da abokan hulɗa yayin da suke magance matsalolin da suka haifar da rashin jin daɗin abokan hulɗa.
MTN ta yi kira ga masu amfani da layukan su kasance masu hakuri kuma su yi amfani da intanet da ake da su don samun tallafi yayin wannan ɗan lokacin na rufe ofisoshi.