Mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), Mallam Nuhu Ribadu, ya ce gwamnatin tarayya na aiki tukuru domin ganin an kubutar da duk wadanda ke tsare a hannun ‘yan bindiga tare da kawo karshen matsalar rashin tsaro a Nijeriya.
Ribadu ya bayyana haka ne a ranar Talata a yayin da ya ke mika wasu iyalai biyar da jami’an tsaro na hadin gwiwa da ke ofishin NSA suka kubutar daga hannun masu garkuwa da mutane.
- Me Ya Kawo Matasa Zuwa Yankin Xizang Na Kasar Sin?
- Kiran Tada Hankali A Zanga-zanga: Rundunar ‘Yansanda Ta Cafke Wani Dan TikTok A Filato
Ribadu ya ce, an yi garkuwa da dukka iyalan Mista Sanda Bitrus da suka hada da matarsa da wani saurayi da ‘ya’yansa uku a ranar 20 ga watan Yulin 2024 a Mahuta da ke karamar hukumar Kaduna ta Kudu a jihar Kaduna.
Ya ce, amma an yi nasarar ceto iyalan ta hanyar hadin gwiwa da ofishin mai bada shawara kan harkokin tsaro na kasa (ONSA) da suka hada da jami’an tsaro daban-daban domin ceto iyalan a ranar 28 ga watan Yuli.
Ribadu ya ce, gwamnatin shugaba Bola Tinubu ta yi alkawarin ganin an kubutar da dukkan ‘yan kasar da ke hannun masu garkuwa da mutane a kowane yanki na kasar nan lafiya.
Ya yabawa jami’an tsaro bisa kwazon da suke yi na kokarin ganin an iya magance matsalolin tsaro a fadin kasar nan.