Rundunar ‘yansandan Nijeriya ta kama wani matashi mai shekaru 34, Suleiman Yakubu, wanda aka yada a wani faifan bidiyo na Tiktok a Filato, yana kira da a yi kone-kone tare da lalata dukiyoyin jama’a a yayin zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa da aka shirya gudanarwa a ranar 1 ga watan Agusta.
Wanda ake zargin, an bi sahunsa ne ta hanyar shafinsa mai suna “Dan_Mallam68,” wanda ya yi kira ga mazauna garin Jos da su kai hari gidajen mai, ofisoshin jami’an tsaro, tare da lalata muhimman ababen more rayuwa na gwamnati da masu zaman kansu a yayin zanga-zangar.
- Zanga-Zanga: Gwamnatin Yobe Ta Bayar Da Umarnin Rufe Makarantun Jihar
- Zanga-zanga: Gwamnatin Nijeriya Ta Hana Zirga-zirga A Hanyoyin Gidajen Gyaran Hali
Daga nan ne jami’an rundunar ‘yansandan jihar Filato da ke Jos suka bibiye shi sannan suka kama shi a ranar Lahadi.
Yayin da yake gabatar da wanda ake zargin a Abuja ranar Talata, ACP Olumuyiwa Adejobi, ya ce, an kama wanda ake zargin ne a ranar 28 ga watan Yuli, kuma a yanzu haka yana hannun ‘yansanda ana gudanar da bincike tare da yi masa tambayoyi.
Talla