Majalisar Wakilai ta umarci kamfanonin Dangote da BUA su bayyana a gabanta don amsa tambayoyi kan zirarewar kudaden harajin Gwamnatin Tarayya.
Kamfanonin simintin BUA da Dangote na cikin jerin kamfanoni masu zaman kansu da cibiyoyin Gwamnatin Tarayya 113 da za su amsa tambayoyi kan wannan lamari.
- Zanga-Zanga: Gwamnatin Yobe Ta Bayar Da Umarnin Rufe Makarantun Jihar
- Zanga-Zanga: NSCDC Ta Shirya Aikewa Da Jami’ai 30,000 Faɗin Nijeriya
Shugaban kwamitin binciken kudaden jama’a na majalisar, Bamidele Salam ne, ya sanar cewa shugabannin kamfanonin ko manyan akantocinsu ne za su hallara domin amsa tambayoyin.
Ya ce binciken zai mayar da hankali ne kan rashin biyan kudaden haraji ga gwamnati, rashin bin ka’idojin da doka ta shimfida wajen biya, da kuma zirarewar kudaden.
Ya ce binciken zai fara ne daga ranar 30 ga watan nan na Yuli zuwa 8 ga Agusta, 2024, kuma majalisar za ta yi tsattsuran hukunci kan duk kamfani ko cibiyar gwamnati da ta ki amsa gayyatar.
Sanarwar ta ce ana bukatar, “kamfanonin su zo da duk takardun da ake bukata.”
Bankunan First Bank, Zenith Bank, Guarantee Trust, Access Bank, Polaris, FCMB, Fidelity da Keystone na cikin masu amsa tambayoyin.
Kazalika kamfanin hakar mai na Shell Develompent Company da kamfanin lemon kwalba 7Up da kamfanin mai na Durbi Oil.
Sauran kamfonin abinci irin su C-Way Food & Beverages da kamfanin madarar Fan Milk da kamfanin Rite Food Ltd; Guinness Nigeria Plc; Pabod Int’l Breweries; Champion Breweries; Agio Power Plant (Kwale Okpai Power Plant); Euro-Global and Disability Plc.
Hukumomi da cibiyoyin gwamnati da za a bincika sun hada da; Ma’aikatar Noma da Samar da Abinci, wadda za a bincika kan zargin karkatar da kudaden tallafin COVID-19.
Sannan za a binciki Cibiyar Yaki da Yaɗuwar Cututtuka ta Kasa (NCDC) kan zargin karkatar da kudaden yaki da COVID-19.
Hukumar Gidan Radio ta Kasa (FRCN) kuma za ta amsa tambayoyi kan zirarewar kudaden shiga ta kafar Remita.
Sai Majalisar Karamar Hukumar Gwagwalada da za ta amsa tambayoyi kan zargin almundahana da rahoton shekarar 2020 da ofishin babban mai binciken kudi na kasa ya bankado.
Sauran da ake zargi a rahoton sun hada da: Ma’aikatar Tsaro, Matatar Mai ta Kaduna, Kamfanin Wutar Lantarki ta Kasa na kuma Hukumar Iskar Gas ta Kasa (NLNG) da Ma’aikatar Sufuri ta Kasa
Akwai kuma Hukumar Kula da Kamfanonin Gwamnati (BPE), Ma’aikatar Kasafi da Tsare-tsare, Jami’ar Sojoji da ke Jihar Borno, Ma’aikatar Ma’adinai, Hukumar Kogin Neja Delta, Ma’aikatar harkokin waje, Ma’aikatar Ilimi da Hukumar Jarabawa ta Kasa (NECO).
Hakazalika akwai Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) da Kamfanin Dillanccin Labaran Njjeriya (NAN) da Hukumar Aikin Dan Sanda da Cibiyar Yaki da Cutar Kuturta da Tarin Fuka da Hukumar Kidaya ta Kasa da sauransu da suka hada jami’o’i da kwalejin ilimi da cibiyoyin lafiya da sauransu.