An gudanar da taron tattaunawa kan “Kara zurfafa gyare-gyare a Sin dama ce ga duniya” da kuma musayar jama’a tsakanin Sin da Masar na shekarar hadin gwiwa a Cairo, babban birnin Masar, a jiya Talata bisa agogon wurin, wanda babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin wato CMG, da ma’aikatar yawon shakatawa da kayayyakin tarihi ta kasar Masar, da kuma ofishin jakadancin kasar Sin dake Masar suka gudanar tare.
A gun taron, baki daga kasashen Sin da Masar sun yi mu’amala mai zurfi da juna kan damar samun ci gaba ga duniya, sakamakon kara zurfafa gyare-gyare a Sin a sabon zamani. Ban da haka, an watsa wani shirin da CMG ya kaddamar mai taken “Sabon nau’i na wayewar dan Adam:Salon zamanintar da kasar Sin” da harshen Larabci a kasar Masar, kuma a ranar har ila yau, an kuma kaddamar da ayyuka da dama a fannonin fina-finai da shirye-shiryen talabijin, da kafofin watsa labarai da kuma al’adu.
Shen Haixiong, mataimakin shugaban hukumar fadakar da al’umma na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana shugaban CMG, ya bayyana cewa, Sin ta kara zurfafa gyare-gyare a kasar, ko shakka babu, zai samar da tabbaci mai kima a cikin duniya mai cike da rudani, da kuma samar da karin damammakin samun ci gaba, da kara kuzarin Sin ga inganta ci gaba da wadatar bil’adama tare. CMG zai yi amfani da taron tattaunawa da musaya tsakanin jama’a na wannan karo a matsayin mafari don kara karfafa mu’amala da hadin gwiwa, da zurfafa fahimtar juna kan wayewar kai, da karfafa da fadada hadin gwiwa mai inganci tsakanin kasashen biyu a fannonin zurfafa gyare-gyare da mu’amalar al’adu tare da bangarori daban daban na Masar, ta yadda za a ba da gudummawar hikima da karfi ga gina al’ummar mai makomar bai daya ta Sin da Masar da al’ummar mai makomar bai daya ta Sin da kasashen Larabawa a sabon zamani. (Safiyah Ma)