Tsoffin mataimakan gwamnoni biyu daga jihar Kebbi da suka hada da Ibrahim K. Aliyu da Mohammed Bello Dantani, sauran masu sauya shekar sun hada da Magajin Rafin Kabi tare da mataimakin shugaban jam’iyyar APC na shiyyar, Alhaji Atiku Alaramma Warrah da sakataren kungiyar na jiha, Abdullahi Mai Unguwa Shanga da wasu 43. ya sauya sheka daga jam’iyyar APC zuwa jam’iyyar PDP.
A jihar Bauchi ma akalla matan APC 5,000 ne suka sauya sheka zuwa PDP. A yayin da suke bayyana goyon bayansu a sakatariyar jam’iyyar PDP da ke Birnin Kebbi, babban birnin jihar a jiya, Aliyu da Kabi sun ce sun bar jam’iyyar APC ne saboda mugun hali da kuma gazawar gwamnatin jihar wajen aiwatar da ayyuka masu ma’ana a jihar.
- Zaben Fidda-Gwanin PDP: Kotu Ta Fara Sauraren Karar Dan Majalisar Argungu/Augie a Kebbi
- PDP Ta Dakatar Da Dan Takararta Na Sanatan Kebbi Ta Tsakiya
Ya kara da cewa “Gwamnati ta yi alkawarin ba mu mukamai a lokacin zaben fidda gwanin da aka kammala na karshe amma ba a mana komai ba,” in ji shi.
Masu sauya shekar sun bayyana cewa babu yadda za a yi jam’iyyar APC ta samu nasara a zaben 2023 mai zuwa a jihar saboda ‘ya’yanta sun rasa kwarin guwiwa a jam’iyyar.
Shugaban jam’iyyar PDP, Alhaji Bello Suru, wanda ya samu wakilcin sakataren jihar, Alhaji Bawa Kalgo, ya yi maraba da su zuwa jam’iyyar tare da ba su tabbacin cewa za a yi musu adalci da zarar sun yi nasarar kafa gwamnati a 2023.
Ya kuma ba su tabbacin cewa jam’iyyar za ta sauya salon shugabancinta idan ta hau mulki. An tarbi wadanda suka sauya shekar ne tare da masu ruwa da tsaki na PDP, Alhaji Abba Aliero, Alhaji Abubakar Atiku Bunu Jega, Alhaji Garba Maidoki Zuru, Alhaji Sani Dododo da dai sauransu.
A zantawarsa da LEADERSHIP, shugabar ‘yan takarar, Fatima Mohammed, ta ce sun kuduri aniyar komawa jam’iyyar PDP ne sakamakon gazawar gwamnatin tarayya karkashin jam’iyyar APC wajen cika alkawuran da ta dauka na fitar da ‘yan Nijeriya daga kangin talauci da yunwa da dai sauransu.