• Leadership Hausa
Thursday, June 1, 2023
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Sana’a Sa’a
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Sana’a Sa’a
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Zaben Fidda-Gwanin PDP: Kotu Ta Fara Sauraren Karar Dan Majalisar Argungu/Augie a Kebbi

by Umar Faruk
10 months ago
in Labarai
0
Zaben Fidda-Gwanin PDP: Kotu Ta Fara Sauraren Karar Dan Majalisar Argungu/Augie a Kebbi
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Babbar kotun tarayya da ke zamanta a birnin Kebbi, ta fara saurarem karar zaben fidda-gwani na jam’iyyar PDP na mazabun kujerar dan majalisar wakilai na kananan hukumomin Argungu da Augie tsakanin Sani Yakubu da Injiniya Garba Haruna.

An shigar da karar ne a gaban kotun karkashin jagorancin  mai shari’a Babagana Ashigar, wanda Sani Yakubu Augie ya shigar da Injiniya Garba Haruna, INEC da PDP domin sauya sunansa bayan ya lashe zaben fidda-gwani na mazabun Argungu/Augie a matsayin dan takarar kujerar dan majalisar tarayya mai neman tsayawa takara a zaben 2023.

  • Abu Zubaydah Da Aka Yi Wa Lakabin “Dadadden Fursuna”
  • An Sallami Osinbajo Daga Asibiti Bayan Yi Masa Tiyata

Lauyan wanda ya shigar da kara, J. J Usman (SAN) da wasu lauyoyi hudu, sun shaida wa kotun cewa sun gabatar da dukkan takardun karar a gaban kotu kuma an bai wa duk wadanda ake kara takardunsu.

Ya kuma ce dangane da kotu a shirye suke su ci gaba da gudanar da kararsu da hujojinsu a gaban kotun.

Har ila yau, lauyan wanda ake tuhuma na farko, Barista Hussaini Zakariya (SAN), wanda ya bayyana tare da wasu lauyoyi guda hudu, ya bayyana cewa su ma sun gabatar da dukkan takardun bayanan kariya tare da amince wa da hidimar ayyukan masu shigar da kara sannan suka bayyana shirinsu kan kare dukkan zarge-zargen da ake yi wa wanda suke kare wa,” in ji shi”.

Labarai Masu Nasaba

Tallafin Mai: Ba A Cimma Matsaya Tsakanin Gwamnatin Tarayya Da NLC Ba

China Ta Yi Alkawarin Ci Gaba Da Kulla Alakar Tattalin Arziki Da Nijeriya

Sai kuma mai kara na biyu da kuma lauya na uku, Barista Godwin Obibike da Barista Nura Bello sun amince da aikin da lauyan wanda ya shigar da karar ya shigar da su sannan kuma sun tabbatar wa kotu kan shigar da nasu takardun kariya.

Da yake gabatar da karar ga kotun, lauyan mai kara Barista J.J Usman (SAN), ya ce yanzu an shigo da al’amura kuma har yanzu shari’ar ta kai ga fara sauraren karar.

Sauran lauyoyin kuma sun yarda cewa a yanzu shari’ar ta balaga don fara sauraron karar da ta dace.

A nata bangaren, kotun ta ce” bayyana kammala sauraren dukkan bangarorin lauyoyin, ta bayyana cewa an dage sauraron karar zuwa ranar 15 ga watan Agusta 2022 don ci gaba da shari’ar.”

Tags: Birnin KebbiDan MajalisaINECKebbiKotuMai Neman TakaraShari'a
ShareTweetSendShare
Previous Post

Abu Zubaydah Da Aka Yi Wa Lakabin “Dadadden Fursuna”

Next Post

Yajin Aikin ASUU: NLC, ASUU da Sauran Kungiyoyi Sun Gudanar Da Zanga-Zangar Lumana A Kebbi

Related

Tallafin Mai: Ba A Cimma Matsaya Tsakanin Gwamnatin Tarayya Da NLC Ba
Manyan Labarai

Tallafin Mai: Ba A Cimma Matsaya Tsakanin Gwamnatin Tarayya Da NLC Ba

5 hours ago
China Ta Yi Alkawarin Ci Gaba Da Kulla Alakar Tattalin Arziki Da Nijeriya
Labarai

China Ta Yi Alkawarin Ci Gaba Da Kulla Alakar Tattalin Arziki Da Nijeriya

6 hours ago
Za Mu Dauki Kwakkwaran Mataki Idan Gwamnati Ta Janye Tallafin Man Fetur —NLC
Manyan Labarai

Za Mu Dauki Kwakkwaran Mataki Idan Gwamnati Ta Janye Tallafin Man Fetur —NLC

7 hours ago
Akwai Wadataccen Mai Da Zai Ishi ‘Yan Kasa Nan Da Kwanaki 30 —NNPCL
Manyan Labarai

Akwai Wadataccen Mai Da Zai Ishi ‘Yan Kasa Nan Da Kwanaki 30 —NNPCL

8 hours ago
Tinubu Ya Gana Da Shugaban EFCC A Fadar Shugaban Kasa
Manyan Labarai

Tinubu Ya Gana Da Shugaban EFCC A Fadar Shugaban Kasa

9 hours ago
Kotu Ta Daure Basarake Shekaru 15 Saboda Garkuwa Da Kansa
Manyan Labarai

Kotu Ta Ba Da Umarnin Kama Dakta Idris Abdulaziz

11 hours ago
Next Post
Yajin Aikin ASUU: NLC, ASUU da Sauran Kungiyoyi Sun Gudanar Da Zanga-Zangar Lumana A Kebbi

Yajin Aikin ASUU: NLC, ASUU da Sauran Kungiyoyi Sun Gudanar Da Zanga-Zangar Lumana A Kebbi

LABARAI MASU NASABA

Ya Dace ‘Yan Siyasan Amurka Su Yi Tunani Kan Kalaman Elon Musk

Ya Dace ‘Yan Siyasan Amurka Su Yi Tunani Kan Kalaman Elon Musk

May 31, 2023
Kasar Sin Ta Bukaci Amurka Ta Samar Da Yanayin Da Ya Dace Na Tattaunawa Tsakanin Rundunonin Sojin Kasashen 2

Kasar Sin Ta Bukaci Amurka Ta Samar Da Yanayin Da Ya Dace Na Tattaunawa Tsakanin Rundunonin Sojin Kasashen 2

May 31, 2023
Sin Na Son Hadin Kai Da Sauran Sassan Kasa Da Kasa A Fannin Nazarin Sararin Samaniya

Sin Na Son Hadin Kai Da Sauran Sassan Kasa Da Kasa A Fannin Nazarin Sararin Samaniya

May 31, 2023
Gudummawar Kasar Sin Ga Aikin Tabbatar Da Zaman Lafiya A Duniya Abu Ne Da Ake Gani A Zahiri

Gudummawar Kasar Sin Ga Aikin Tabbatar Da Zaman Lafiya A Duniya Abu Ne Da Ake Gani A Zahiri

May 31, 2023
Tallafin Mai: Ba A Cimma Matsaya Tsakanin Gwamnatin Tarayya Da NLC Ba

Tallafin Mai: Ba A Cimma Matsaya Tsakanin Gwamnatin Tarayya Da NLC Ba

May 31, 2023
Sin Na Goyon Bayan Gwamnatin Mali Wajen Yaki Da Ta’addanci Da Tabbatar Da Tsaron Kasa

Sin Na Goyon Bayan Gwamnatin Mali Wajen Yaki Da Ta’addanci Da Tabbatar Da Tsaron Kasa

May 31, 2023
An Gudanar Da Taro Karo Na 12 Na Dandalin Masanan Sin Da Afirka

An Gudanar Da Taro Karo Na 12 Na Dandalin Masanan Sin Da Afirka

May 31, 2023
China Ta Yi Alkawarin Ci Gaba Da Kulla Alakar Tattalin Arziki Da Nijeriya

China Ta Yi Alkawarin Ci Gaba Da Kulla Alakar Tattalin Arziki Da Nijeriya

May 31, 2023
Za Mu Dauki Kwakkwaran Mataki Idan Gwamnati Ta Janye Tallafin Man Fetur —NLC

Za Mu Dauki Kwakkwaran Mataki Idan Gwamnati Ta Janye Tallafin Man Fetur —NLC

May 31, 2023
Akwai Wadataccen Mai Da Zai Ishi ‘Yan Kasa Nan Da Kwanaki 30 —NNPCL

Akwai Wadataccen Mai Da Zai Ishi ‘Yan Kasa Nan Da Kwanaki 30 —NNPCL

May 31, 2023
Advertise with us

© 2022 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2022 Leadership Media Group - All Right Reserved.