Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya karyata rahotannin sanya dokar hana fita a jihar biyo bayan wawure dukiyar gwamnati da wasu bata-gari suka yi a babban birnin jihar a yayin zanga-zangar adawa da kunci da yunwa a jihar.
Gwamna Sani, wanda ya bayyana hakan a shafinsa na Facebook a ranar Alhamis da yamma, ya bayyana cewa, komai na karkashin ikon gwamnati.
- Tura Ta Kai Bango, Zanga-zanga Ta Kai Gidan Buhari Da Sarkin Daura
- Ɓata-gari Sun Cinna Wa Sakatariyar APC Wuta Tare Da Lalata Kadarorin Gwamnati A Jigawa
Gwamnan ya rubuta cewa, “Ba a sanya dokar hana fita ba a Kaduna. Komai yana karkashin ikon gwamnati a yanzu.”
A baya mun rahoto cewa, wasu bata-gari sun kutsa cikin masu zanga-zangar adawa da kuncin rayuwa a ranar Alhamis sun bankawa wani bangare na ofishin Hukumar Kula da Dokokin Sufuri ta Jihar Kaduna (KASTLEA) wuta tare da kwashe wasu kadarori na hukumar.
Sun kuma lalata wani bangare na ginin hedikwatar hukumar bunkasa zuba jari ta Kaduna (KADIPA).