Sabanin bukatun masu zanga-zangar #EndBadGovernance da ke ci gaba da gudana, Shugaba Bola Tinubu ya ce, ba zai yi wu ba a maido da biyan tallafin man fetur.
Shugaban kasar a wani jawabi da ya yi wa ‘yan Nijeriya a safiyar ranar Lahadi, ya bayyana cewa, duk da cewa matakin cire tallafin man fetur ya haifar da tsanani da kuncin rayuwa, amma hakan ya zama dole domin biyan tallafin ba ya haifar da alkairi ga tattalin arzikin kasarmu sai dai kawo cikas ga ci gaban tattalin arzikinmu da ci gabanmu.”
- Jan Aikin Da Ke Gaban Sababbin Shugabannin Kano Pillars
- Mummunan Tasirin Da Kuncin Rayuwa Ke Yi Ga Al’umma Wajen Bin Addini
Shugaban ya kuma shaida wa masu zanga-zangar cewa, jami’an tsaro za su ci gaba da tabbatar da cikakken tsaron rayuka da dukiyoyin ‘yan kasa ta hanyar da ta dace, inda ya kara da cewa, “Dimokuradiyyarmu tana ci gaba ne idan aka mutunta da kuma kare hakkokin da tsarin mulki ya ba kowane dan Nijeriya.
Shugaba Tinubu ya bayyana cewa, “Manufar da nake da ita game da kasarmu, ita ce, a samu kasa mai adalci da wadata, inda kowane mutum zai ci moriyar zaman lafiya, ’yanci, da rayuwa mai arha wacce ba tsada wanda shugabanci nagari na dimokuradiyya ne kadai zai iya samar da ita – shugabanci irin na Dimokuradiyya a bayyane yake, da gaskiya da rikon amana ga al’ummar Nijeriya.
“Tsawon shekaru da yawa, tattalin arzikinmu ya kasance mai rauni, kuma mara karsashi, saboda rashin daidaituwa da yawa da suka kawo cikas ga ci gabanmu. Sama da shekara guda da ta wuce, kasarmu Nijeriya, ta kai matsayin da ba za mu iya ci gaba da yin amfani da hanyoyin magance matsalolin wucin gadi don magance matsalolin da dole mu kawo karshensu ba, domin kanmu da kuma zuriyarmu masu zuwa daga baya.
“Saboda haka na dauki matsaya mai raɗaɗi wacce ta zama dole na cire tallafin man fetur da kuma kawar da tsarin musayar kuɗi da yawa wacce ke haifar da rudani da cikas ga ci gaban tattalin arzikinmu da ci gabanmu.”
“Wadannan shawarwarin da na yanke sun zama dole idan har muna so mu ceto tattalin arzikin kasarmu daga durkushewa. Eh, na yarda, kuɗin kasa yana tsayawa akan teburi na. Amma ina tabbatar muku cewa, na mayar da hankali sosai wajen jagoranci nagari ga jama’a” In ji Tinubu