Wata takardar aiki da aka fitar a ranar Asabar ta bayyana cewa, kasar Sin za ta yi kokarin kara bunkasa sassan ba da hidima ga masu bukata, don tallafawa ci gaban tattalin arziki mai inganci, da biyan bukatun jama’a game da hidimomi na musamman, a fannoni daban daban, kuma masu inganci.
Takardar, wadda majalisar gudanarwar kasar Sin ta fitar, ta zayyana muhimman ayyuka guda 20, da suka hada da yin amfani da damammakin dake tattare da sassan ba da hidima kamar su tarbar baki, hidimar gida, kula da tsoffi, kula da yara, nishadi, yawon bude ido, wasanni, ba da ilimi da horo.
- Gwamnati Ta Bai Wa Gwamnoni Fiye Da Naira Biliyan 570 Don Tallafa Wa Talakawa – TinubuÂ
- Jan Aikin Da Ke Gaban Sababbin Shugabannin Kano Pillars
Kasar Sin za ta fadada bukatun cikin gida tare da mai da hankali kan kara yin sayayya, kuma biyan kudi don samun hidima zai zama babban ginshiki wajen fadadawa da inganta sayayya, a cewar wani muhimmin taron tsara muhimman manufofi na rabin karshe na shekarar 2024 a kwanan baya.
Alkaluma sun nuna cewa, a cikin watanni 6 na farkon bana, yawan kudade da aka kashe a bangaren hidimomi a kasar Sin ya karu da kashi 7.5 cikin dari, idan aka kwatanta da na makamancin lokaci na shekarar da ta gabata, kuma ya fi yawan kudaden da aka kashe kan hajoji yawa har kashi 4.3 cikin dari. (Yahaya)