A jiya Asabar, masu zanga-zanga a jihar Kano sun nemi shugaban ƙasar Rasha, Vladimir Putin, ya sa baki, suna daga tutar Rasha a bisa fusatar rashin kulawa da koke-kokensu daga gwamnatin shugaban ƙasa Bola Tinubu. Wannan ya faru ne a rana ta uku ta zanga-zangar tsadar rayuwa wato #EndBadGovernance da aka yi kan tsananin yunwa da talauci a Najeriya.
Zanga-zangar ta rikiɗe ta zama tashin hankali, inda ta haifar da rikici tsakanin wasu ‘yan daba da jami’an tsaro, wanda ya janyo mutuwar mutane da dama da raunata wasu.
- Shugaban Kasa Yana Bibiyar Zanga-zangar Matsin Rayuwa – Minista
- Tsadar Rayuwa: Atiku Ya Yi Allah Wadai Da Harbin Masu Zanga-zanga
Shaidu sun ruwaito cewa rikicin ya fara ne lokacin da matasa suka saɓa dokar hana fita da jihar ta ƙaƙaba don ci gaba da zanga-zangar a yankunan Rijiyar Lemo, da Kurna zuwa Bachirawa, da Kofar Nasarawa, da Unguwa Uku.
Abdulkadir Musa, mazaunin Rijiyar Lemo, ya bayyana cewa an harbe a ƙalla mutane takwas, ciki har da mata da yara, tare da tabbatar da mutuwar tsohuwa da wasu mutane uku. An ce ƴan dabar sun yi ƙoƙarin fasa shaguna suna fakewa da zanga-zangar yunwa, wanda ya haifar da ƙarin tashin hankali da raunuka.
Masu amfani da kafofin sada zumunta sun yi wallafe wallafe game da tarzomar, suna nuna yadda ƴansanda suka yi amfani da ƙarfi don tarwatsa masu zanga-zangar.
Rundunar Ƴansanda ta jihar Kano ba ta yi ƙarin haske kan rahotannin kisan ba, lamarin da ya janyo ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta. Ƙoƙarin tuntubar mai magana da yawun rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, bai yi nasara ba saboda ba a iya samun sa ta waya.