A ƙoƙarin tabbatar da tsaron rayuka da kiyaye doka da oda, Gwamnan Jihar Filato, Barr. Caleb Manasseh Mutfwang, ya sanya dokar hana fita ta awa 24 kan yankin Jos/Bukuru, wanda zai fara aiki daga karfe 12 na daren yau Lahadi, 4 ga watan Agusta, 2024.
Wannan shawarar, wadda aka yanke tare da haɗin gwuiwar hukumomin tsaro na jihar, ta zo ne sakamakon ayyukan ɓata gari yayin zanga-zangar ƙasa baki ɗaya. Wasu mutane dauke da makamai sun yi amfani da damar, suka fasa shaguna da gidajen ajiye abinci a kan titin Bauchi da mararrabar Zololo.
- Ginin Makaranta Ya Rufta A Jos, Ɗalibai Da Dama Sun Maƙale
- Tsohon Ministan Buhari Ya Shiga Zanga-Zanga A Jos
Gwamna Mutfwang ya jaddada cewa dokar hana fitar tana da muradin tabbatar da zaman lafiya, tare da yin kira ga mutane da su yi biyayya domin tabbatar da tsaro. An umurci hukumomin tsaro da su tabbatar da an bi dokar ta hana fita sosai. Gwamnan ya gargadi waɗanda ke shirin tada fitina su kiyaye ko su fuskanci fushin doka. Haka kuma, ya yi kira ga hukumomin tsaro da su kasance cikin shiri don hana duk wani rashin tsaro.