Yanzu haka Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya kulle ƙofa don gudanar da taro da shugabannin hukumomin tsaro da a Fadar Shugaban ƙasa da ke Abuja. Wannan taro na gaggawa, wanda aka shirya ƙarƙashin majalisar tsaro ta ƙasa ya biyo bayan ɗage taron majalisar zartarwa ta ƙasa (FEC) da aka tsara gudanarwa a yau Litinin.
Taron yana gudana ne tare da jagorancin Shugaban ma’aikatan tsaro, Janar Christopher Musa, tare da manyan shugabannin Sojoji da sauran manyan jami’an tsaro.
- Tuntuni Muka Yi Gargaɗin Cewa, Zanga-zanga Za Ta Iya Zama Hargitsi – Minista Idris
- Zanga-zanga: Majalisar Tsaro Ta Sanya Dokar Hana Fita Ta Sa’o’i 24 A Kaduna
Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, da shugaban ma’aikata na shugaban ƙasa, da Femi Gbajabiamila, da Sufeto Janar na Ƴansanda Kayode Egbetokun duk suna halartar taron.
Wannan taron dai yana gudana ne a yayin da ake ta zanga-zangar matsin rayuwa a fadin ƙasa.
Zamu kawo muku cikakken bayani nan gaba kan yadda ta wakana.