Gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad ya ƙaƙaba dokar hana zirga-zirga na tsawon awa 24 a ƙaramar hukumar Katagum da ke jihar sakamakon taɓarɓarewar lamarin tsaro a garin Azare da kewayenta.
Idan za a tuna dai mun bada labarin da ke cewa masu zanga-zangar neman dawo da tallafin mai da kawo karshen matsin rayuwa rayuwa a ranar Litinin sun kutsa kai cikin sakatariyar karamar hukumar da ke Azare da gidan Gwamnatin jihar Bauchi (masaukin baki) da ke Azare tare da gidan tsohon mataimakin gwamnan jihar Baba Tela inda suka yi satar wasu kayayayyaki da ƙone-ƙone a wasu yankunan gami da lalata kadarori.
- Jan Aikin Da Ke Gaban Sababbin Shugabannin Kano Pillars
- Ba Wanda Zai Yi Zanga-zanga A Bauchi – Muhammad Ibrahim
A wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar Bauchi, Ibrahim Muhammad Kashim ya fitar a yau Litinin, na cewa, gwamnatin ta ɗauki wannan matakin ne sakamakon matsalolin tsaro da aka samu a Azare da kewayenta da ya janyo lalata kadarori jama’a da cin zarafi.
Gwamnan ya umarci hukumomin tsaro da su tabbatar da sun zaƙulo waɗanda suka saci kayan al’umma domin su fuskanci hukunci.
Ya ce, “Mai girma gwamna Sanata Bala Abdulkadir Mohammed ya amince da sanya dokar hana zirga-zirga ta tsawon awanni 24 a ƙaramar hukumar Katagum kuma dokar za ta fara aiki ne nan take domin daƙile lamarin.”