ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Fasahar Zamani Na Taka Rawar Gani Ga Ci Gaban Masana’antu Sin

by Sulaiman and CGTN Hausa
2 years ago
Sin

Tarihi ya nuna cewa ana iya kaucewa takunkumi ko kuma takunkumin ya zama wata hanyar samar da damammaki ga kasa. Kamar dai yadda takunkumin da Washington ta kakkabawa kayayyakin kasar Sin a shekarar 2023, ya zama wata albarka ga kasar, wanda ya karawa kasar saurin samun bunkasa bisa manyan tsare-tsare.

Takunkumin da Amurka ta kakkabawa kasar Sin ya karkatar da hankalin kasar zuwa ga raya masana’antun gargajiya, da noma da masana’antu na kiwon lafiya bisa manyan fasahohin zamani da kirkirarriyar basira wato AI. Tare da goyon baya mai muhimmanci daga gwamnati da al’ummomin ’yan kasuwa, da masana kimiyya na kasar Sin da masu bincike wadanda suka hada kirkirarriyar basirar AI da 5G wajen gudanar da ayyukan masana’antu tare da sassan tattalin arziki masu alaka da kere-kere, da samar da kayayyaki da hidimomi masu karko. Fitattun kamfanoni irin su Alibaba, Tencent da Huawei da masana’antar motocin lantarki da na wutar lantarki bisa sabbin makamashi da sauransu, sun taka muhimmiyar rawa a wannan sauyi na fasaha.

ADVERTISEMENT
  • Jirgin Saman C919 Kirar Kasar Sin Ya Fara Zirga-zirga Kan Hanya Ta 5 
  • Sin Ta Gaggauta Raya Tsarin Yaki Da Balaun Ambaliyar Ruwa Da Fari

Ana iya danganta bunkasuwar fasahohin kasar Sin musamman ga matakin da gwamnati ta dauka da hangen nesa kan dabarun tsara manufofi game da zuba jari a fannin fasaha. Samun nasarar bunkasa amfani da AI ba wai kawai ya kara daukaka matsayin kasar Sin a fagen masana’antun duniya ba, har ma ya karfafa tasirinta a masana’antar fasaha ta duniya.

LABARAI MASU NASABA

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

Wannan tunanin ya haifar da yanayin da kamfanonin Sin ke iya gogayya kafada da kafada da wasu manyan kamfanonin fasahar zamani na duniya, da kuma taka muhimmiyar rawa ta hanyar hadin gwiwa da kirkire-kirkire wadanda suka kasance jigon masana’antar kere-kere ta kasar Sin, wanda kuma ke baiwa dukkan masu ruwa da tsaki a fannin kwarin gwiwar samun ci gaba da kuma karfin da suke da shi.

An kara fayyace ci gaban masana’antar kere-kere ta kasar Sin ta hanyar bunkasar tattalin arzikinta na dijital, yayin da a shekarar 2023, adadin darajar kayayyaki na manyan masana’antu a cikin tattalin arzikin dijital ya kai kashi 10 cikin 100 na GDPn kasar.

Wannan nasarar ta cimma burin ci gaban tattalin arzikin dijital na “tsarin shekaru biyar-biyar” karo na 14 wato daga 2021 zuwa 2025, shekaru biyu ke nan gabanin jadawalin. Nasarorin da aka samu sun nuna saurin bunkasuwar fasahohin kasar Sin don inganta karfinta a masana’antar fasaha ta duniya. (Mohammed Yahaya)

Sin
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna
  • Sulaiman
    Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba
  • Sulaiman
    Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa
  • Sulaiman
    Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina Kasa
Sin
CGTN Hausa
+ posts Bio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Xi Jinping Ya Taya Kim Jong-Un Murnar Cika Shekaru 78 Da Kafuwar Koriya Ta Arewa
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

MASU ALAKA

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna
Daga Birnin Sin

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

September 9, 2026
Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba
Daga Birnin Sin

Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

September 9, 2026
Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa
Daga Birnin Sin

Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

September 9, 2026
Next Post
Yaduwar Fasahar Juncao Ta Nuna Sahihancin Sin

Yaduwar Fasahar Juncao Ta Nuna Sahihancin Sin

LABARAI MASU NASABA

Sin

Jerin Bankuna 32 Da Aka Amince Su Sayar Da Hannun Jarin Matatar Dangote

September 10, 2026
Sin

Uganda Za Ta Fara Fitar Da Man Fetur Zuwa Ƙasashen Waje

September 10, 2026
Cutar Mashaƙo Ta Ɓarke A Kano, Katsina Da Filato

Mashaƙo: Adadin Mutanen Da Suka Rasu Sun Kai 27 A Filato

September 10, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

Wane Ne Dan Shagamu: Su Wane Ne Suka Kashe Shi A Kano?

September 10, 2026
Al’umma Sun Yaba Wa Sojoji Kan Yaƙar ’Yan Bindiga A Zamfara

Al’umma Sun Yaba Wa Sojoji Kan Yaƙar ’Yan Bindiga A Zamfara

September 10, 2026
Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

September 10, 2026
’Yansanda Sun Kama Wadda Ta Yaɗa Labarin OPay Zai Daina Aiki A Nijeriya

’Yansanda Sun Kama Wadda Ta Yaɗa Labarin OPay Zai Daina Aiki A Nijeriya

September 10, 2026
2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

September 10, 2026
Zabe: Gwamnatin Kano Ta Taƙaita Zirga-zirgar Mutane Da Ababen Hawa

Gwamna Yusuf Ya Umarci Jami’an Tsaro Su Gano Waɗanda Suka Kashe Danshagamu

September 10, 2026
Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

September 9, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.