Gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammad ya nuna takaicinsa kan yadda wasu suka duƙafa wajen yaɗa jita-jitar cewa ya na aikin gina Gadoji ne domin tono Gwala-Gwalai don sayarwa wasu ‘Yan China.
Ya ce, abun kunya ne a ce har da wasu manyan mutane ake yaɗa irin wannan labarin ƙanzon kuregen na cewa Gwal suke tonowa.
- Zanga-zanga: Bauchi Ta Yi Hannun Riga Da Ikirarin Rufe Asibitoci
- Da Dumi-Dumi: Gwamnatin Bauchi Ta Sanya Dokar Hana Fita Na Awa 24 A Katagum
Bala Muhammad ya shaida haka ne a daren yau Litinin yayin da ya kira taron gaggawa na majalisar tsaron jihar domin neman mafita kan zanga-zangar da matasa ke yi kan matsin rayuwa.
Bala ya ce su na aikin gina Gadoji guda biyu a kasuwar Wunti da Central ne domin rage cinkoso da ingata zirga-zirga, don haka ne ya shawarci jama’a da su daina sauraron jita-jita balle ma su yaɗa ta.
Tun da farko, gwamnan ya ce, an shiga wani hali a Nijeriya, sai ya nuna cewa ba lokaci ne na ɗaura ma wani shugaba ko wasu laifi ba, ya ce a matsayinsu na shugabanni dole dukkaninsu su ɗauki lamarin domin neman mafita.
A cewarsa, gwamnatinsa ta gudanar da shirye-shirye da dama na taimakon matasa da samar da ayyukan yi, duk da haka ya ce yanzu lokaci ne na neman yadda za a cire jama’a daga cikin halin matsin rayuwa.
A gefe guda ya nemi matasa da su kauce wa tashin tashina.