ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ambaliyar Ruwa Ta Lalata Kasuwar Dodoru A Jihar Kebbi, Rumfuna Da Yawa Sun Lalace

by Umar Faruk Birnin Kebbi
2 years ago
Ambaliya

Wata mummunar ambaliyar ruwa ta afkawa kasuwar Dodoru da ke ƙaramar hukumar Gwandu a jihar Kebbi, inda ta lalata shaguna da rumfuna sama da 51, Kasuwar wadda ita ce ɗaya daga cikin babbar hanyar samar da kuɗaɗen shiga ga jihar, tana jan hankalin dubban ‘yan kasuwa da kwastomomi daga sassan yankin a duk ranar Litinin.

Ambaliyar ruwan wadda ta afku a yau Litinin, ta bar Kasuwar cikin rugujewa, inda ‘yan kasuwa da dama suka yi asarar duniyoyinsu da kuma sauran wasu Kayayyakinsu na Miliyoyin Nairori.

Haka kuma kayan abinci, da wasu sassan kasuwar sun samu mummunar illa, inda buhunan taki, da gishiri, da sauran kayan amfanin gona suka lalace.

ADVERTISEMENT
  • An Yi Wa Matashi Daurin Rai Da Rai Kan Yi Wa Kurma Fyade A Kebbi
  • Hukumar SEMA Ta Jihar Kebbi Ta Tallafa Wa Mutanen Da Ambaliyar Ruwan Sama Ta Shafa A Argungu

‘Yan kasuwa da kwastomomi suna ta kokawa game da ambaliyar, sakamakon asarar da mata tafka, kamar yadda wani dan Kasuwa wanda ya nemi a sakaye sunansa ya ce “Na yi asarar sama da buhunan gishiri 60 da sauran kayayyaki,” in ji wani ɗan Kasuwa. “Ban san yadda zan farfaɗo daga wannan halin ba.”

Ambaliya

LABARAI MASU NASABA

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue

Shugaban ƙungiyar ‘yan Kasuwar, Alhaji Bello Aliyu Gwandu, ya roƙi gwamnatin jihar da ta taimaka wa ‘yan Kasuwa kan wannan ambaliyar ruwan da ta sanya ‘yan Kasuwarmu asarar dukiyarsu “Wannan Kasuwa ita ce jigon rayuwar al’ummarmu, muna  buƙatar taimako don sake farfadowa,” inji shi.

Kasuwar Dodoru wani muhimmin bangare ne na tattalin arzikin yankin, inda ake samun kuɗaɗen shiga a kowane mako. Rushewarta zai haifar da rashin aiki da taɓarɓarewar tattalin arziki da asara mai yawa ga al’umma da kuma jihar.

Ambaliya
Umar Faruk Birnin Kebbi
+ postsBio
  • Umar Faruk Birnin Kebbi
    https://hausa.leadership.ng/author/umar-faruk-birnin-kebbi/
    Gwamnan Kebbi Ya Buƙaci Sojoji Su Ƙara Kaimi Wajen Fatattakar Ƴan Bindiga
  • Umar Faruk Birnin Kebbi
    https://hausa.leadership.ng/author/umar-faruk-birnin-kebbi/
    Ƙungiyar Ƙwadago A Kebbi Ta Nemi Mafi Ƙarancin Albashin Na ₦500,000
  • Umar Faruk Birnin Kebbi
    https://hausa.leadership.ng/author/umar-faruk-birnin-kebbi/
    Ƴan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Alƙalin Babbar Kotu A Kebbi
  • Umar Faruk Birnin Kebbi
    https://hausa.leadership.ng/author/umar-faruk-birnin-kebbi/
    Kungiyar Malaman Jami’ar AFUSTA Za Ta Tsunduma Yajin Aiki

MASU ALAKA

Ballon D'or
Manyan Labarai

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

September 8, 2026
Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue
Manyan Labarai

Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue

September 8, 2026
2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi
Manyan Labarai

2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi

September 8, 2026
Next Post
Zanga-zanga: Daga Tutar Rasha Cin Amanar Kasa Ne – Janar Musa

Zanga-zanga: Daga Tutar Rasha Cin Amanar Kasa Ne - Janar Musa

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.