Gwamnatin jihar Nasarawa ta amince da biyan naira 70,000 a matsayin mafi karancin albashil ga Ma’aikatan Jihar.
Gwamnan jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule ya amince da biyan 70,000 a matsayin mafi karancin albashi.
- Tuni Tallafin Man Fetur Ya Dawo – Obasanjo
- Masu Shigo Da Mai Za Su Kawowa Matatar Dangote Cikas – Obasanjo
Da yake zantawa da manema labarai, mai taimakawa Gwamnan kan harkokin yada labarai, kwamared Piter Ahemba yace, tuni Gwamnan Abdullahi Sule ya amince da kuddurin Gwmnatin tarayya na biyan naira 70,000 a matsayin mafi karancin albashi.
Ahemba ya kara da cewa; Gwamnan Abdullahi Sule baya wasa da biyan albashin Ma’aikatan Gwamnati tun kasancewarsa a matsayin gwamnan jihar Nasarawa.
Ya ce, Gwamnan ya kuma kara daukar sabbin Ma’aikatan Gwamnati a bangaori daban-daban.
“Gwamnan Abdullahi Sule yanzu haka yana aikin gina katafariyar Sakatariyar bai-daya da za ta hada dukkan Ma’aikatun Gwamnatin waje guda.
“Gwamnan ya kuma gina tituna a biranai da karkara a fadin jihar.” In ji Kwamared Ahemba.