Gwamnatin Zamfara ta karyata jita-jitar da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa ta ware Naira biliyan 19 don saya wa Gwamna Dauda Lawal kayan girki.
Kwamishinan Kasafin Kudi da Tsare-tsaren Tattalin Arziki na Jihar, Abdulmalik Gajam, ya bayyana wannan labarin a matsayin labarin kazon kurege a wani taron manema labarai da aka yi a Gusau.
- Tinubu Ya Binciki Kuɗaɗen Da Yake Bai Wa Gwamnoni – Sheikh Yakubu Musa
- Kamala Harris Ta Zabi Tim Walz A Matsayin Mataimaki Kafin Shiga Zaben Amurka
Gajam, ya bayyana cewa, bayanan da ake yadawa ba su da tushe, face son bata sunan gwamnan jihar.
Ya bayyana cewa, gwamnatin jihar ta mayar da hankali wajen rage zurarewar kudi.
Ya bukaci kafafen yada labarai da sauran masu ruwa da tsaki suke tabbatar da sahihancin bayanai kafin yadawa.
Yayin da yake jaddada aniyar gwamnatin na kasancewa mai gaskiya, Gajam ya gayyaci manema labarai su bincika tare da tabbatar da gaskiyar lamarin.
Ya yi gargadi cewa, yadawa irin wadannan bayanai marasa tushe na iya jefa jama’ar Zamfara cikin rudani.
Gajam, ya kuma sake jaddada manufofin kasafin kudin 2024, wanda ke mayar da hankali wajen samar da karin kudaden shiga, rage kashe kudi, da kuma tabbatar da gaskiya wajen fitar da kudaden jama’a.
Ya tabbatar da cewa dukkanin kudaden da gwamnati ke kashewa a yanzu yana amfanar da jama’ar jihar.