Jam’iyyar PDP ta Jihar Kebbi ta sanar da janyewa daga shiga zaben kananan hukumomin da aka shirya gudanarwa a ranar 31 ga watan Agusta, 2024.
Da yake zantawa da manema labarai, Shugaban jam’iyyar, Alhaji Bello Usman Suru, ya bayyana dalilai guda uku da ya dogara da su kan yanke wannan shawarar, kamar haka:
1- Shugabannin da ke jagorancin Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar (KESIEC), dukkansu ‘yan jam’iyyar APC ne, lamarin da ke nuna damuwa kan yadda hukumar za ta iya gudanar da sahihin zabe na gaskiya da adalci.
2- Biyan kudaden gudanarwa ga ’yan takara da jam’iyyun siyasa suke yi, abin da PDP ke ganin ya saba wa ‘yancin zabe da kuma dokar gudanar da zabe.
3- Haka kuma, Canjin shugabannin Hukumar KESIEC ba zato ba tsammani daga ranar 30 ga watan Agusta zuwa 7 ga watan Agusta, wanda jam’iyyar ke kallon wani yunkuri ne na hana jam’iyyun adawa shiga zaben kananan Hukumomin.
Don haka, Shugaban jam’iyyar PDPn ya jaddada cewa, shiga zaben zai nuna amincewa da tsarin da acewar jam’iyyar, ba yi shi bisa ka’ida ba.
Ya kuma yi kira ga ‘ya’yan jam’iyyar da su kwantar da hankulansu yayin da jam’iyyar ke ci gaba da sa ido kan abubuwan da ke faruwa tare da fatan hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) za ta dauki nauyin gudanar da zabukan kananan hukumomi.