• English
  • Business News
Saturday, October 18, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamnatin Tinubu Na Ƙoƙarin Gyara Kurakuran Baya, Ba Jawo Wahala Ba – Minista

by Sulaiman
1 year ago
Tinubu

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ce, babban abin da gwamnatin Tinubu ta fi mayar da hankali a kai ba shi ne ta ɗora wa ‘yan Nijeriya wahala ba, sai dai ta gyara munanan tsare-tsare da matakan da ba su dace ba waɗanda a tarihi suka kawo cikas ga ci gaban Nijeriya.

A wata sanarwa da Mataimakin Ministan na Musamman kan Harkokin Yaɗa Labarai, Rabi’u Ibrahim, ya fitar,  Ministan ya bayyana haka ne a Abuja a ranar Laraba yayin da yake ganawa da jami’an diflomasiyya a Ma’aikatar Harkokin Wajen Ƙasar dangane da zanga-zangar da aka yi a faɗin ƙasar.

  • Gwamnan Gombe Ya Bayar Da Umurnin Raba Kayan Abinci Don Rage Raɗaɗin Kuncin Rayuwa
  • Gwamnatin Filato Ta Sassauta Dokar Hana Fita A Jihar

Ya jaddada ƙudirin Shugaba Tinubu na aiwatar da gyare-gyare da nufin samar da ci gaba mai ɗorewa da kuma inganta rayuwa ga ɗaukacin ‘yan ƙasa, yana mai cewa, ƙalubalen da ake fuskanta a yanzu na wucin-gadi ne.

LABARAI MASU NASABA

JIBWIS FCT Ta Yi Taron Yaye Iyaye Mata Da Suka Kammala Koyon Sana’o’i

An Fara Yi Wa Yara Miliyan 1.6 Rigakafi A Taraba

Ministan ya ce, “Yana da muhimmanci mu fara da wannan bayanin cewa, Shugaba Tinubu bai zo ofis don ya jawo wahalhalu ko kuma wahalar da ’yan Nijeriya ba. Ya zo ne don warware matsalolin baya; tare da yunƙurin gyara da yawa daga cikin tsare-tsaren da ba su da kyau da kuma matakan da ba su dace ba da suka kawo mana koma-baya a matsayin mu na ƙasa shekaru da yawa.

Tinubu

“Shugaban Ƙasa ya hau karagar mulki ne a ɗaya daga cikin lokuta mafi ƙalubale a tarihin Nijeriya, inda ƙasar ke kashe kashi 97 na dukkan kuɗaɗen shigarta wajen biyan basussuka; tare da yawaitar talauci, hauhawar rashin aikin yi, lalacewar ababen more rayuwa, da rashin tsaro. Yayin da take fuskantar waɗannan abubuwa masu ban tsoro, gwamnati ta ɗauki ƙwararan matakai tare da aiwatar da gyare-gyaren da aka daɗe ba a yi ba domin ceto tattalin arziƙin ƙasar daga durƙushewa.”

Ministan ya bayyana cewa kawar da tallafin man fetur ya zama dole don karkatar da kuɗaɗen zuwa sassa masu muhimmanci kamar kiwon lafiya, ilimi, ababen more rayuwa, da tsaro, wanda ke tasiri kai tsaye ga jin daɗin ’yan ƙasa da ci gaban ƙasa.

Ya amince da cewa ana shan raɗaɗin sauyin da ke tattare da wannan matakin kuma ya yi nuni da cewa Gwamnatin Tarayya ta tsara shirye-shiryen shiga tsakani don magance waɗannan ƙalubale.

“Mun dage sosai kan tabbatar da cewa an aiwatar da waɗannan ayyukan domin kawo sassauci ga ‘yan Nijeriya,” inji Idris.

Yayin da yake magana kan zanga-zangar da aka gudanar a faɗin ƙasar nan, ministan ya ce gwamnati na mutunta ‘yancin yin taro cikin lumana da ‘yancin faɗin albarkacin baki, waɗanda su ne ginshiƙin dukkan al’ummomin dimokiraɗiyya, amma ya jaddada cewa abin da ya fara a matsayin zanga-zangar lumana a wasu jihohi da kuma Babban Birnin Tarayya shi ne ba da jimawa ba wasu da suka kutsa kai cikin zanga-zangar suka karɓe ragamar tare da shirya tarzomar da ta lalata rayuka da dukiyoyi.

“An samu rahotannin ƙone-ƙone, ɓarna, sace-sace, da kuma arangama da jami’an tsaro a garuruwa da dama. Abin takaici, waɗannan al’amura sun yi sanadin asarar rayukan da ba su ji ba ba su gani ba da kuma asarar dukiya mai yawa,” inji shi.

Idris ya tabbatar wa da jami’an diflomasiyya cewa Gwamnatin Tarayya ta fara gudanar da bincike kan tashe-tashen hankulan da aka yi a lokacin zanga-zangar domin a gano tare da gurfanar da duk masu hannu a cikin lamarin.

Ya ce: “Mun himmatu wajen hana sake aukuwar irin wannan mummunan lamari a nan gaba.”

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

JIBWIS FCT Ta Yi Taron Yaye Iyaye Mata Da Suka Kammala Koyon Sana’o’i
Labarai

JIBWIS FCT Ta Yi Taron Yaye Iyaye Mata Da Suka Kammala Koyon Sana’o’i

October 18, 2025
An Fara Yi Wa Yara Miliyan 1.6 Rigakafi A Taraba
Labarai

An Fara Yi Wa Yara Miliyan 1.6 Rigakafi A Taraba

October 18, 2025
Ƴansanda Sun Kama Gungun Masu Sojan Gona Suna Aikata Laifuka A Kano
Labarai

Ƴansanda Sun Kama Gungun Masu Sojan Gona Suna Aikata Laifuka A Kano

October 18, 2025
Next Post
Jami’in Kenya: Taron Dandalin FOCAC Zai Zurfafa Dangantakar Sin Da Kenya

Jami’in Kenya: Taron Dandalin FOCAC Zai Zurfafa Dangantakar Sin Da Kenya

LABARAI MASU NASABA

Mataimakin Firaministan Sin Ya Zanta Da Sakataren Baitul-mali Da Wakilin Cinikayyar Amurka

Mataimakin Firaministan Sin Ya Zanta Da Sakataren Baitul-mali Da Wakilin Cinikayyar Amurka

October 18, 2025
JIBWIS FCT Ta Yi Taron Yaye Iyaye Mata Da Suka Kammala Koyon Sana’o’i

JIBWIS FCT Ta Yi Taron Yaye Iyaye Mata Da Suka Kammala Koyon Sana’o’i

October 18, 2025
‘Yansanda Sun Cafke Ɓarayi 13 Tare Da Ƙwato Shanu 27 A Kaduna

Gwamnatin Jihar Taraba Ta Ayyana Yi Wa Kasuwannin Sayar Da Dabbobi 9 Garanbawul

October 18, 2025
Iwobi Na Dab Da Kafa Tarihi A Gasar Firimiya

Iwobi Na Dab Da Kafa Tarihi A Gasar Firimiya

October 18, 2025
Dalilin Bankin AfDB Na Yin Hadaka Da WFP Da IFPRI

Dalilin Bankin AfDB Na Yin Hadaka Da WFP Da IFPRI

October 18, 2025
An Fara Yi Wa Yara Miliyan 1.6 Rigakafi A Taraba

An Fara Yi Wa Yara Miliyan 1.6 Rigakafi A Taraba

October 18, 2025
Lewandowski Ba Zai Buga Wasan El Classico Ba

Lewandowski Ba Zai Buga Wasan El Classico Ba

October 18, 2025
Ƴansanda Sun Kama Gungun Masu Sojan Gona Suna Aikata Laifuka A Kano

Ƴansanda Sun Kama Gungun Masu Sojan Gona Suna Aikata Laifuka A Kano

October 18, 2025
Ƴan Bindiga Sun Kai Hari Ofishin Ƴansanda, Sun Kashe 2 A Kaduna

Ƴan Bindiga Sun Kai Hari Ofishin Ƴansanda, Sun Kashe 2 A Kaduna

October 18, 2025
Radda

Gwamnan Katsina Ya Bukaci Al’umma Su Hada Hannu Da Gwamnati Wajen Kawar Da Matsalar Tsaro

October 18, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.