Shugaban hukumar kula da makamashi ta kasar Sin Zhang Jianhua, ya ce Sin za ta iya cimma nasarar kaiwa ga kololuwar fitar da sinadarin carbon, tare da fara rage fitar da shi ya zuwa shekarar 2030, duk kuwa da kalubalen makamashi da ake fuskanta a duniya.
Zhang Jianhua, wanda ya bayyana hakan a jiya Laraba, ya ce duk da kalubale na karancin makamashi da ake fama da shi a duniya, da sake bude tashoshin samar da makamashi daga kwal a sassan Turai, a nata bangare, kasar Sin na nacewa manufar samar da makamashi daga abubuwan da ba dangogin fetur ba.
A bara, makamashin da aka yi amfani da shi a Sin da ba dangogin fetur ba sun karu, daga kaso 15.9 zuwa kaso 16.6. Zhang ya kara da cewa, akwai hasashen karuwar adadin da kaso 1 bisa dari a duk shekara har zuwa shekarar 2030.
Jami’in ya kuma yi karin haske game da ci gaban da Sin ta samu, a fannin gina cibiyoyin cajin ababen hawa masu amfani da sabbin makamashi, yana mai cewa, ya zuwa shekarar 2025, Sin za ta samar da irin wadannan cibiyoyi da za su wadatar da sama da ababen hawa masu amfani da lantarki har miliyan 20. (Mai fassarawa: Saminu Alhassan daga CMG Hausa)