Wasu Matasa a garin Demsa da ke ƙaramar hukumar Demsa a jihar Adamawa sun daka warwaso kan wata tirelar taki da gwamnatin jihar ta tura zuwa ƙaramar hukumar Demsa, yayin da motar ta je sauke takin a fadar mai martaba Hama Bata Alhamdu Teneke.
Wannan lamari dai ya faru ne sakamakon rashin wurin ajiyar kayan, (Store), da ƙaramar hukumar ba ta da shi, inda motar ke ƙoƙarin kai takin gidan Sarkin, sai kuma ta faɗa cikin kwalbati, a lokaci guda kuma, matasan suka fara warwason.
- An Kama Mutane 2 Da Laifin Kashe Wani Mutum Kan ‘Maita’ A Adamawa
- ECOWAS Ta Bada Tallafin Kayan Abinci Ga Mutane 12,000 Da Ambaliyar Ruwa Ta Shafa A Adamawa
Shugaban ƙaramar hukumar Demsa, Hon Akam Sanda Jallo ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kuma zargi dillalin kai takin da rashin sanar da shi tafiyar da suka yi na kai takin fadar Hama Batta domin ajiyewa.
Ya ce dillali mai sayar da takin da ke kula da Yola a fadar jihar, ya kamata ya jira sai ya ba shi umarnin tafiya kafin su tashi zuwa Demsa.
Sai dai ya ce suna da wani babban wanda ake zargi da laifin tura yaran wajen wawashe takin da ake son rabawa manoman yankin a wannan lokaci na damina.
Akam ya ƙaryata raɗe-raɗen da ake yaɗawa cewa waɗanda suka wawure takin matasa ne masu zanga-zangar #endbadgoverent ne suka yiwa motar kwanton ɓauna a fadar Hama Bata, ya ce ba haka bane a kwai wanda su ke zargi da tura matasan, amma bai bayyana ko waye ba.
Ya bayyana cewa motar ta maƙale ne kuma ta fadi sakamakon rashin kyawun hanya, a nan ne matasan suka yi warwason kayan suka yi awon gaba da su.
Wasu majiyoyin tsaro sun tabbatar da cewa jami’an tsaro sun cafke wasu matasan da ake zargi da warwason takin zamanin jiya Juma’a.