Hukumar Kula da Shige da Fice ta Nijeriya, NIS a ranar Litinin ta ce ta fara gudanar da bincike sakamakon yada wani faifan bidiyo a shafukan sada zumunta, da ke nuna wata matafiya na yayyaga fasfo din Nijeriya a filin jirgin sama na Murtala Mohammed (MMIA), Legas.
Jami’in hulda da jama’a na hukumar, DCI Kenneth Udo ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Abuja.
- ‘Yan Bindiga Fiye Da 30 Sun Mutu Sakamakon Rikici A Tsakaninsu A Zamfara
- Gwamnatin Tinubu Na Ƙoƙarin Gyara Kurakuran Baya, Ba Jawo Wahala Ba – Minista
Ya ce, an binciko matar kuma an gayyace ta don ci gaba da bincike da amsa tambayoyi.
“Idan har an tabbatar da zargin da ake yi mata, lallai aikinta ya sabawa sashe na 10 (b) na dokar shige da fice ta shekarar 2015 (wacce aka gyara), za kuma a hukuntata kamar yadda doka ta tanada a karkashin sashe na 10 (h) na wannan dokar.
“NIS za ta ci gaba da tsayawa tsayin daka wajen tabbatar da tanade-tanaden dokar shige-da-fice domin kare martabar kasa, da kuma kare mutuncin ka’idojin shari’a na kasa,” inji shi.