Ministar Masana’antu, Kasuwanci da Zuba Jari, Dr. Doris Uzoka Anite ta bayyana cewa, asarar dukiyoyin da aka yi sakamakon zanga-zangar #EndBadGovernance a Nijeriya ta kai Naira biliyan 500.
A cikin wata sanarwa da ta fitar a shafinta na X, ta kuma yi jimamin asarar rayuka da sauran barnar da zanga-zangar ta haifar.
- Zanga-zangar Tsadar Rayuwa Ta Haifar Da Karancin Man Fetur A Nijeriya
- Gwamna Bago Ya Yi Allah-wadai Da Kona Coci A Neja
A cewarta, an lalata kayayyaki kusan na Naira biliyan 52, yayin da adadin wadanda suka mutu a zanga-zangar ya kai 21.
Ta yi nuni da cewa, wawure dukiyar jama’a da wasu bata-gari acikin masu zanga-zangar suka yi, wani koma baya ne ga kasuwanci da ‘yan kasuwa a fadin kasar nan.
Talla