• English
  • Business News
Monday, July 28, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Daya Daga Fasinjojin Jirgin Kasan Kaduna Zuwa Abuja: Dalilin Sakin Faifan Bidiyon Azabtar Da Mu – Barista Hassan

by Shehu Yahaya
3 years ago
in Manyan Labarai
0
Barista Hassan
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram
  • Ba Na Fatan Ko Makiyina Ya Shiga Hannun Masu Garkuwa
  • Na Yi Ido Biyu Da Daya Cikin Wadanda Suka Fasa Gidan Yarin Kuje

BARRISTA HASAN LAWAL USMAN, na daya daga cikin mutane ukun da ‘yan ta’adda suka sako a ranar Litinin ta makon nan. Wakilinmu a Kaduna SHEHU YAHAYA ya garzaya gidansa da ke Unguwar Rimi a cikin karamar hukumar Kaduna ta Arewa inda ya tattauna da shi a kan irin darasin da ya dauka yayin zamansu a hannun masu garkuwa da mutane.

Daga cikin abin da ya bayyana a tattaunawar, akwai dalilin sakin faifan bidiyon da aka nuna ana ta dukan su a karshen mako wanda ya haifar da shakku a kan al’amarin tsaron al’ummar kasar baki daya. Ya ce duk da shakar iskar ‘yancinsa, har yanzu yana cikin damuwa saboda halin da sauran mutanen da aka sace a jirgin kasan Abuja zuwa Kadunan ke ciki a daji bayan kwashe watanni hudu.

Hakika wakilinmu ya tarar da shi cikin yanayi da jimami da tausayi tare da murna lamarin da ya sanya yana magana yana zubda hawaye bisa ganin yadda jama’a suka yi dafifi a kofar gidansu domin taya shi murnar dawowa gida.

Duk da yawan jama’a da suke gidan, Usman Hassan, ya dan ba mu lokaci a gurgije domin amsa wasu tambayoyi da muka yi masa inda a ciki ya bayyana cewa ba zai iya gane mazaunin da aka ajiye su ba, amma ba ya fatan ko makiyinsa ya kasance a irin halin da suka tsinci kansu a ciki.

Ka da mu cika ku da dogon bayani. Ga yadda hirar ta kasance:
Barrista Hasan Lawal Usman, ga shi ka fito daga hannun masu garkuwa da mutane, shin ya kake ji?
Alhamdu lillah! Magana ta gaskiya yanzu ga ni ina zaune cikin murna tare ‘yan’uwana da abokan arziki suna taya ni murna bisa irin halin da na samu kaina a ciki. Ina godiya ga Allah sosai.

Labarai Masu Nasaba

SDP: Fadar Shugaban Ƙasa Ta Yi Wa El-Rufai Shaguɓe Da Ayyana Shi A Matsayin Ɗan Gudun Hijirar Siyasa

Sojoji, DSS Sun Hallaka Ƴan Bindiga 45 A Neja

Wanne irin yanayi suka ajiye ku yayin zaman ku a hannunsu?
Na farko dai, sun ajiye mu a wani kungurmin daji, inda a nan ne muke kwana a kasa daga nan sai muka samu wani abin shinfida muke shinfudawa a kasan bishiya muke kwanciya. Lokacin da aka fara ruwan sama suka yi mana wasu ‘yan rumfuna da zarar sun ga hadari ya taso, sai su kai mu ciki mu kwana. Amma gaskiya zaman wurin babu dadi ko daya domin ko makiyanka ka da ka yi masa fatan ya kasancewa a wurin.

Wasu sun ce sai da ‘yan’uwanku suka biya kudin fansa kana aka sako ku, ya abin yake?
Ammm! Gaskiya ba zan iya cewa an biya kudi ko ba a biya kudi ba kamin aka sako mu. Abin da na sani shi ne, ‘yan’uwa da abokan arziki sun yi yunkurin fitowa da mu, saboda gwamnati Nijeriya ta gaza a kan nauyin da ta daukar wa kanta na kare rayuwarmu da dukiyoyinmu.
‘Yan’uwanmu suka shiga cikin wannan halin suka je suna neman hanyar da za su fito da mu, amma mun samu labarin cewa gwamnati ta hana su su wuce domin su kubuto da mu, wanda jami’an tsaron suka hana su wucewa, sai dai duk da haka suka kara dawowa domin kubuto da mu, wanda yanzu ga shi sun samu nasarar kubutar da mu.

Toh! Ku nawa aka sako a wannan karon?
Eh! Mu uku ne, maza biyu sai mace guda daya.

Kamar ku nawa ne aka tsare a dajin?
Akalla mun kai arba’in (40).

Amma gaba daya ku nawa aka kama?
Mu sittin da hudu (64) ne.

Yanzu idan aka ce ka koma dajin, shin za ka iya gane dajin da aka ajiye ku?
Gaskiya ba zan iya ganewa ba.

Ko akwai wani yunkuri da kake ganin jami’an tsaro sun yi wajen kubutar da ku?
Gaskiya ba ni da wata masaniya a kan wani yunkurin da jami’an tsaro suka yi wajen kubutar da mu. Na san dai ranar Juma’a mu ukun da aka sako mun zo wurin da za a karbe mu, sai muka samu labarin cewa jami’an tsaro sun hana a fito da mu. Abin da na sani kenan.

Toh! Barista yaya batun abincin da kuke ci a dajin?
Gaskiya suna iya bakin kokarinsu wajen ba mu abinci daidai karfinsu. Wani lokacin har shanu suke yanka mana da awakai. Hatta ranar da aka sako mu sai da suka yanka mana sanuwa aka ba mu muka ci.

Ina gaskiyar labarin da muka samu na cewa wasu daga cikin ‘yan Boko Haram da suka fasa gidan yarin Kuje duk sun dawo dajin da kuke zama?
Eh! Gaskiya ne! Na yi ido biyu da daya daga cikinsu, saboda akalla akwai mutanensu kamar guda shida zuwa tara da suka dawo cikin dajin tare da ‘yan’uwansu, saboda a faifan bidiyon da aka aiko akwai guda daya da yake ikirarin cewa yana daga cikin wadanda suka kubuta daga gidan yarin Kuje.

Ina batun duka, an ce kullum suna lakada muku duka?
Gaskiya tun da muka je babu wanda ake duka har sai lokacin da wannan abun ya harzuka gwamnati, sannan suka fara dukanmu kamar yadda aka aiko a faifan bidiyon da aka turo. Gaskiya mun sha duka mutuka kuma sun ce wannan ma somin-tabi ne. Yanzu ma ina cikin jimamin halin da sauran ‘yan’uwa suke ciki, domin za su kasance cikin mummunar yanayi muddin dai ba a kawo musu dauki ba. Muna kira ga Gwamnatim Nijeriya da na kashen ketare da su taimaka su ceto sauran mutanan da suke tsare a cikin dajin.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Martanin Babban Hafsan Soja Ga ‘Yan Ta’adda: Karshenku Ya Zo

Next Post

Dan KAROTA Ya Samu Kyautar Miliyan 1 Kan Kin Karbar Cin Hanci Daga Direbobin Motar Giya

Related

Kakakin Majalisar Wakilai, Abbas, Ya Yi Jimamin Rasuwar Buhari, Ya Ce Mutuwa Ce Da Ta Girgiza Shi
Da ɗumi-ɗuminsa

SDP: Fadar Shugaban Ƙasa Ta Yi Wa El-Rufai Shaguɓe Da Ayyana Shi A Matsayin Ɗan Gudun Hijirar Siyasa

1 hour ago
Sojoji, DSS Sun Hallaka Ƴan Bindiga 45 A Neja
Manyan Labarai

Sojoji, DSS Sun Hallaka Ƴan Bindiga 45 A Neja

3 hours ago
Harin Sojojin Sama Ya Hallaka Manyan Shugabannin ISWAP A Borno
Manyan Labarai

Harin Sojojin Sama Ya Hallaka Manyan Shugabannin ISWAP A Borno

6 hours ago
Shetima Zai Wakilci Nijeriya A Taron Tsarin Abinci A Addis Ababa
Manyan Labarai

Shetima Zai Wakilci Nijeriya A Taron Tsarin Abinci A Addis Ababa

1 day ago
Nijeriya Ta Lashe Gasar Kofin Nahiyar Afirika Ta Mata 
Wasanni

Nijeriya Ta Lashe Gasar Kofin Nahiyar Afirika Ta Mata 

2 days ago
Duk Da Ni Ɗan Adawa Ne Buhari Ya Hana A Murɗe Min Zaɓe — Dickson
Siyasa

Duk Da Ni Ɗan Adawa Ne Buhari Ya Hana A Murɗe Min Zaɓe — Dickson

2 days ago
Next Post
Dan KAROTA Ya Samu Kyautar Miliyan 1 Kan Kin Karbar Cin Hanci Daga Direbobin Motar Giya

Dan KAROTA Ya Samu Kyautar Miliyan 1 Kan Kin Karbar Cin Hanci Daga Direbobin Motar Giya

LABARAI MASU NASABA

Ana Ci Gaba Da Habaka Karfin Kudin Kasar Sin Tun Daga Shekarar 2021

Ana Ci Gaba Da Habaka Karfin Kudin Kasar Sin Tun Daga Shekarar 2021

July 28, 2025
Sin Ta Samar Da Manyan Manhajojin AI Sama Da 1500

Sin Ta Samar Da Manyan Manhajojin AI Sama Da 1500

July 28, 2025
Kakakin Majalisar Wakilai, Abbas, Ya Yi Jimamin Rasuwar Buhari, Ya Ce Mutuwa Ce Da Ta Girgiza Shi

SDP: Fadar Shugaban Ƙasa Ta Yi Wa El-Rufai Shaguɓe Da Ayyana Shi A Matsayin Ɗan Gudun Hijirar Siyasa

July 28, 2025
Sojoji, DSS Sun Hallaka Ƴan Bindiga 45 A Neja

Sojoji, DSS Sun Hallaka Ƴan Bindiga 45 A Neja

July 28, 2025
SDP Ta Kori Tsohon Gwamnan Kaduna El-Rufai

SDP Ta Kori Tsohon Gwamnan Kaduna El-Rufai

July 28, 2025
Harin Sojojin Sama Ya Hallaka Manyan Shugabannin ISWAP A Borno

Harin Sojojin Sama Ya Hallaka Manyan Shugabannin ISWAP A Borno

July 28, 2025
Ministan Yaɗa Labarai Ya Yi Jimamin Rasuwar Babban Ɗan Jarida Leon Usigbe

Ministan Yaɗa Labarai Ya Yi Jimamin Rasuwar Babban Ɗan Jarida Leon Usigbe

July 28, 2025
Ƴansanda Sun Cafke Barayin Motoci 3 A Kano

Ƴansanda Sun Cafke Barayin Motoci 3 A Kano

July 28, 2025
Tinubu Ya Ƙaddamar Da Shirin Bai Wa Malaman Manyan Makarantun Nijeriya Rancen Miliyan 10

Tinubu Ya Ƙaddamar Da Shirin Bai Wa Malaman Manyan Makarantun Nijeriya Rancen Miliyan 10

July 28, 2025
An Kwashe Duk Dabbobin Tsohon Akanta-Janar

An Kwashe Duk Dabbobin Tsohon Akanta-Janar

July 28, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.