Kwamitin kolin JKS da majalisar gudanarwar kasar, sun fitar da wasu ka’idoji da burikan kare muhalli a jiya Litinin, wato zuwa 2030, kasar za ta cimma nasarori a fannin sauya akala zuwa ci gaba maras gurbata muhalli, a dukkanin fannonin raya tattalin arziki da zamantakewar al’umma. Kana zuwa 2035, ta cimma burin fitar da iskar carbon mafi karanci.
Batun sauyin yanayi wani muhimmin batu ne da ya addabi duniya. Kuma kasar Sin ta kasance gaba-gaba wajen ganin tabbatuwar muradin duniya na shawo kan sauyin yanayi ta hanyoyi daban-daban, duk kuwa da cikas din da wasu ke kawowa wannan yunkuri.
- Tawagar JKS Ta Halarci Bikin Rantsar Da Shugaban Kasar Rwanda
- Anya Nahiyar Afirka Fili Ne Na Gudanar Da Takara?
Hakika ni ganau ce na irin nasarorin da Sin take samu wajen neman ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba. Daga lokacin da na zo kasar zuwa yanzu, na ga yadda a wani lokaci a da can, sararin samaniya ke dusashewa saboda hayakin masana’antu, amma zuwa yanzu, wannan ya zama labari, domin kwata-kwata sararin samaniya a washe take a ko da yaushe, inda na kan yi mamakin yadda a hankali a hankali aka samu wannan gagarumin sauyi. Baya ga wannan, kasar Sin na kokarin kare muhalli da yaki da hayakin carbon ta hanyar shuka bishiyoyi, domin na gani da idona yadda hamada ta zama dausayi. Haka kuma na ga yadda ababen hawa masu amfani da makamashi mai tsafta ke mamaye titunan kasar a hankali.
Hakika dabarun da kasar Sin take amfani da su abun burgewa ne da koyi. Misali, yayin da ake rajin shuka bishiyoyi, ana karfafawa mutane gwiwar shuka bishiyoyi masu samar da kudin shiga, domin samun riba biyu. Haka kuma yayin da ake raya masana’antar ababen hawa masu amfani da makamashi mai tsafta, an tanadarwa jama’a rangwame wajen sayen irin wadannan motoci, har ma a wasu yankuna, a kan ba da damar sauya tsoffin motoci masu amfani da man fetur da masu amfani da lantarki kan farashi mai rahusa.
Sai dai kuma duk da wannan yunkuri da irin ci gaba na a zo a gani da take samu, maimakon a yaba ko a yi koyi da ita, wasu kasashe na kokarin kawo cikas. Amma a tunanina, cikas din da suke kawowa ba ga kasar Sin ba ne, cikas ne ga duniya da za su iya amfana da dabaru da kayayyakin kasar Sin masu kare muhalli. Kuma ina da yakinin cewa, kasar Sin ta yi a gaba a wannan fanni, kana matakan kariyar cinikayya ba za su hana zuwa wadancan shekaru da Sin ta dibarwa kanta, ta cimma burinta na sauyawa baki daya, zuwa ga samun ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba.