• English
  • Business News
Thursday, November 6, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Minista Ya Buƙaci Hukumomi Da Ma’aikatu Kan Yin Aiki Tuƙuru Dan Kishin Ƙasa

by Sulaiman
1 year ago
Minista

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya rattaba hannu kan yarjejeniyar yin aiki tuƙuru tare da shugabannin hukumomi da ƙungiyoyin da ke ƙarƙashin ma’aikatarsa.

Ministan ya umarce su da su yi aiki wurjanjan domin yaɗa bayanai kan nasarorin Shirin Sabunta Fata na Shugaban Ƙasa Bola Tinubu.

  • Shirin 3MTT Zai Samar Wa Matasa Miliyan Uku Aikin Yi, inji Ministan Yaɗa Labarai
  • Kungiyar Likitoci Ta Kasa Ta Yi Barazanar Tsunduma Yajin Aiki Kan Sace Abokiyar Aikinsu

Idris ya yi wannan kiran ne a Abuja ranar Talata yayin da yake buɗe taron kwana ɗaya na Daraktocin Ma’aikatar da shugabannin hukumomin ta da cibiyoyin ta.

LABARAI MASU NASABA

Yadda Gwamna Lawal Ya Aiwatar Da Ayyukan Gina Zamfara Na Naira Biliyan 140

Majalisa Ta Amince Da Ɗaurin Shekaru 14 A Gidan Yari Ga Malamai Masu Cin Zarafin Mata A Jami’o’i

Ya ce, “Tun zuwan gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, akwai tsarin da aka yi don cimma Shirin Sabunta Fata tare da dukkanin ma’aikatu da hukumomi, tare da kuma na’urar bin diddigi don tabbatar da ɗa’a. Sashen Bayarwa da Gudanar da Sakamako (CRDCU) a ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya ne ke sarrafa na’urar bin diddigin.

“Dukkan ku a nan kuna da alhakin kai sakamakon mu ga wannan ofishi a matsayin shugabanni ko Jami’an Bayarwa. An shirya wannan taro ne don tabbatar da cewa mun fahimci wannan alhakin.

“Za ku iya tuna cewa ni da Babbar Sakatariya mun rattaba hannu kan yarjejeniyar aiki tuƙuru tare da Shugaban Ƙasa don tabbatar da cewa za mu aiwatar da aikin ma’aikatar. An gaya mani cewa Babbar Sakatariya ta sa daraktoci su ma su jajirce wajen aiwatar da aikin.

“A yayin wannan taron, na yi ƙudiri aniyar samun shugabannin hukumomi su sanya hannu kan yarjejeniyar aiki tuƙuru su ma.”

Ministan ya bayyana cewa akwai buƙatar shugabannin hukumomin yaɗa labarai da sassan ma’aikatar su fahimci ƙoƙarin gwamnati na shirin Sabunta Fata. Wannan ya haɗa da haɓaka mafi ƙarancin albashi, lamunin ɗalibai, rance na mabuƙaci, lamunin kasuwanci, da tallafi daban-daban, ta yadda za su iya isar da bayanai kan waɗannan ga jama’a yadda ya kamata.

“Har ila yau, gwamnati ba ta bar ayyukan ta na samar da ababen more rayuwa da ayyukan jama’a a faɗin ƙasar nan ba; dole ne mu fahimci wannan yunƙurin kafin mu iya yaɗa su cikin nasara,” inji shi.

Idris ya ce ayyukan ma’aikatar har ila yau sun haɗa da ayyukan da suka shafi tsari da haɗa kai da sauran hukumomin gwamnati don yaɗa bayanan ayyukan su.

Ya buƙaci mahalarta taron da su tattauna game da wuraren da ba su da tabbas don tabbatar da cewa ba wai kawai sun aiwatar da aikin su tuƙuru ba, a’a har ma a riƙa ganin sun yi hakan yadda ya kamata.

Idris ya kuma miƙa godiyar sa ga Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara ta Musamman kan Tsare-tsare, Hadiza Bala Usman, bisa yadda ta nuna sha’awar ta kan wannan aiki, ya kuma yaba da irin kyakkyawan aikin da tawagar ta ke yi a CRDCU.

Mahalarta taron sun haɗa da Babbar Sakatariyar Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Dakta Ngozi Onwudiwe; Darakta Janar na hukumar talabijin ta NTA, Comrade Abdulhameed Dembos; Darakta Janar na Hukumar Kula da Gidajen Talabijin da Rediyo ta Ƙasa (NBC), Mista Charles Ebuebu; Darakta Janar na Hukumar Rediyon Tarayyar Nijeriya (FRCN), Dakta Mohammed Bulama; Darakta Janar na gidan rediyon Muryar Nijeriya (VON), Malam Jibrin Baba Ndace; Manajan Darakta na Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN), Alhaji Ali Mohammed Ali, Sakatariyar Zartaswa ta Majalisar Jarida ta Nijeriya, Dakta Dili Ezughah; da daraktoci a ma’aikatar, da sauran su.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Yadda Gwamna Lawal Ya Aiwatar Da Ayyukan Gina Zamfara Na Naira Biliyan 140
Labarai

Yadda Gwamna Lawal Ya Aiwatar Da Ayyukan Gina Zamfara Na Naira Biliyan 140

November 5, 2025
Majalisar Dattawa
Labarai

Majalisa Ta Amince Da Ɗaurin Shekaru 14 A Gidan Yari Ga Malamai Masu Cin Zarafin Mata A Jami’o’i

November 5, 2025
Dantsoho Ya Nemi Hadin Kan Kasashen Afrika Wajen Bunkasa Tashoshin Jiragen Ruwa
Labarai

Dantsoho Ya Nemi Hadin Kan Kasashen Afrika Wajen Bunkasa Tashoshin Jiragen Ruwa

November 5, 2025
Next Post
Kasar Sin Na Tir Da Harin Isra’ila Kan Makarantu A Gaza Tare Da Kira Da A Dakatar Da Bude Wuta

Kasar Sin Na Tir Da Harin Isra’ila Kan Makarantu A Gaza Tare Da Kira Da A Dakatar Da Bude Wuta

LABARAI MASU NASABA

Mao Ning: Harka Da Kasar Sin Mabudi Ne Na Samun Damammaki

Mao Ning: Harka Da Kasar Sin Mabudi Ne Na Samun Damammaki

November 5, 2025
Yadda Gwamna Lawal Ya Aiwatar Da Ayyukan Gina Zamfara Na Naira Biliyan 140

Yadda Gwamna Lawal Ya Aiwatar Da Ayyukan Gina Zamfara Na Naira Biliyan 140

November 5, 2025
Li Chenggang Ya Gana Da Tawagar Cinikayyar Kayan Noma Ta Amurka

Li Chenggang Ya Gana Da Tawagar Cinikayyar Kayan Noma Ta Amurka

November 5, 2025
Majalisar Dattawa

Majalisa Ta Amince Da Ɗaurin Shekaru 14 A Gidan Yari Ga Malamai Masu Cin Zarafin Mata A Jami’o’i

November 5, 2025
Yanayi Mai Launin Zinare A Kasar Sin

Yanayi Mai Launin Zinare A Kasar Sin

November 5, 2025
Dantsoho Ya Nemi Hadin Kan Kasashen Afrika Wajen Bunkasa Tashoshin Jiragen Ruwa

Dantsoho Ya Nemi Hadin Kan Kasashen Afrika Wajen Bunkasa Tashoshin Jiragen Ruwa

November 5, 2025
Nazarin Cgtn: Kasashe Masu Tasowa Sun Yi Kira Da A Inganta Tsarin Tafiyar Da Harkokin Duniya

Nazarin Cgtn: Kasashe Masu Tasowa Sun Yi Kira Da A Inganta Tsarin Tafiyar Da Harkokin Duniya

November 5, 2025
Gwamna Yusuf

Malam Triump: Ƙungiyoyin Ɗariƙun Sufaye Sun Maka Gwamnan Kano A Kotu

November 5, 2025
An Rufe Canton Fair Na 138 A Guangzhou

An Rufe Canton Fair Na 138 A Guangzhou

November 5, 2025
Sabbin Ministoci

Majalisa Ta Nuna Damuwa Kan Rahoton Yiwuwar Asarar Dala Biliyan 300 A Badaƙalar Ɗanyen Mai

November 5, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.