Mutane 16 ne suka rasu, 3,986 suka rasa matsugunansu yayin da fiye da hekta 2,744 na gonaki suka lalace sakamakon ambaliyar ruwa da ta mamaye kauyuka a fadin kananan hukumomi 10 na jihar Jagawa.
Idan ba a manta ba, hukumar kula da yanayin sararin samaniya ta Nijeriya (NiMet) ta yi hasashen yiwuwar samun ambaliyar ruwa sosai a wasu jihohi a wannan shekara.
- Kungiyar Likitoci Ta Kasa Ta Yi Barazanar Tsunduma Yajin Aiki Kan Sace Abokiyar Aikinsu
- Shirin 3MTT Zai Samar Wa Matasa Miliyan Uku Aikin Yi, inji Ministan Yaɗa Labarai
Sakataren zartarwa na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar (SEMA), Dakta Haruna Mariga, ne ya bayyana haka a lokacin da yake bayar da cikakken bayani game da iftila’in ambaliyar ruwan da ta mamaye kananan hukumomi 10 na jihar.
Mariga ya bayyana cewa, duk da cewa damina ba ta kai kololuwarta ba, amma asarar da aka samu ya zuwa yanzu na da matukar tayar da hankali, saboda fargabar lamarin na iya ta’azzara ganin yadda ruwan ke ci gaba da karuwa.
Shugaban SEMA ya bayyana cewa, gwamnatin jihar tare da hadin gwiwar hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa NEMA sun fara raba kayan agaji da suka hada da kayan abinci ga wadanda lamarin ya shafa.