Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya amsa tambayoyin manema labarai a yau Laraba 14 ga wata. Game da rahoton da ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta fitar, mai taken “Asusun ba da tallafin dimokradiyya na NED: Abun da ya kunsa da kuma abun da ya yi”, Lin Jian ya ce, rahoton mai kunshe da kwararan shaidu, ya tona asirin asusun NED bisa hujjar “samar da ci gaba ga dimokradiyya da kare hakkin dan Adam”, inda a cewarsa, babu wata kasa da ta cancanci ta maida kanta malamar sauran kasashe a fannin kare hakkin dan Adam, kana, bai kamata a kawo illa ga muradun sauran kasashe ba, ta hanyar fakewa da batun “daukaka ci gaban dimokradiyya da kare hakkin dan Adam”.
Game da hadin-gwiwar kasashen Amurka, da Birtaniya da Australiya a fannin jirgi karkashin ruwa mai amfani da makamashin nukiliya kuwa, jami’in ya ce, kafin sassan kasa da kasa sun cimma matsaya dangane da batun samar da tabbaci da sa ido kan wannan batu, bai dace kasashen uku su yi irin wannan hadin-gwiwa ba. (Murtala Zhang)