Rundunar ‘yansanda ta kama wasu ‘yan uwa guda biyu da laifin birne wani matashi dan shekara 16 da ransa a kan bacewar wata waya a garin Zaria na jihar Kaduna.
Wannan al’amari mai ban al’ajabi, wanda ya yadu a kafafen sada zumunta, ya kuma harzuka jama’a inda da dama ke Allah-wadai da matakin. Hakan ya jawo hankalin mahukuntan jihar, wanda ya kai ga cafke wadanda suka aikata laifin.
- Shirin Tsaftace Ruwa Na Sin Ya Lashe Lambar Karramawa Ta Kasa Da Kasa A Fannin Kirkire Kirkire
- Gwamnonin Nijeriya Sun Aminta Da Salon Mulkin Tinubu
Mummunan lamarin ya faru ne a unguwar Gauraki da ke gundumar Kufaina, a karamar hukumar Zariya ta jihar. Sun birne matashin dan shekara 16 mai suna Abubakar da ransa bayan an zarge shi da satar wayar hannu.
Kwamishiniyar ayyuka da jin dadin jama’a ta jihar, Hajiya Rabi Salisu, ta ce, lamarin ya yi matukar tayar da hankali, inda ta jaddada cewa wadanda ake zargin dole sai an hukuntasu.