Majalisar koli ta kasa da kungiyar gwamnonin Nijeriya, sun jaddada amincewarsu ga salon shugabancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Gwamnan Jihar Kwara AbdulRahman AbdulRazak, wanda shi ne shugaban kungiyar gwamnonin, ya shaida hakan ga manema labarai a ranar Talata jim kadan bayan ganawa daban-daban da bangarorin biyu suka yi da shugaba Tinubu.
- Nijeriya Ta Fara Sayar Da Makaman Da Ta Ke Kerawa – Minista
- Nazarin CGTN Ya Bayyana Yadda Wasu Mutanen Duniya Suka Soki EU Game Da Takkadamar Cinikayya Tsakaninta Da Sin
Wannan na zuwa ne kwanaki bayan zanga-zangar adawa da yunwa da matsin rayuwa a kasar.
Majalisar kolin dai, ta kunshi tsofaffin shugabannin Nijeriya, zababbu da na mulkin soja, da gwamnoni, da ministoci, da shugabannin majalisar tarayya wanda suka gana da shugaban Tinubu.
Daga bisani kungiyar gwamnoni ta yi nata ganawar, inda suke tattauna halin da kasa ke ciki da kuma matakan da ya kamata a dauka.
Cikin tsofaffin shugabannin da suka halarci zaman har da Muhammadu Buhari da Goodluck Jonathan da Abdulsalami Abubakar da Yakubu Gowon, sai dai tsohon shugaban kas, Olusegun Obasanjo bai halarci taron ba.
Majalisar ta kan yi zama ne a duk lokacin da wani muhimmin batu ya taso, domin bayar da shawarar yadda za a magance shi.
Wannan dai shi ne karon farko da Shugaba Tinubu ya jagoranci taron tun bayan hawansa mulki a watan Mayun 2023.