Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta jihar Kano (KANSIEC) ta yanke Naira miliyan 10 ga ‘yan takarar da ke neman kujerar shugaban karamar hukuma yayin da ‘yan takarar kansiloli za su biya Naira miliyan 5 gabanin zaben kananan hukumomin jihar da za a yi a ranar 30 ga watan Nuwamba.
Shugaban KANSIEC, Farfesa Sani Lawan Malumfashi, ne ya bayyana hakan a yayin gabatar da dokokin zabe da jadawalin ayyuka ga wakilan jam’iyyun siyasa a hedikwatar hukumar a ranar Alhamis.
- Sin Na Shirin Amfani Da Fasahohin Dijital Wajen Bunkasa Magungunan Gargajiya Na Kasar
- Shekaru 60: DICON Ta Taimaka Wajen Samar Mana Da Makamai – Janar Musa
Ya yi bayanin cewa, dan takarar da zai tsaya takarar shugaban karamar hukuma dole ne ya biya Naira miliyan 10 yayin da dan takarar kansila zai biya Naira miliyan 5.
Malumfashi ya bayyana cewa, ka’idojin sun bayyana dukkan batutuwan da suka shafi cancanta da kuma akasinta don tsayawa takara.
Ya ce, ka’idojin sun kunshi abin da bai kamata a aikata ba a yayin gudanar da zaben, yana mai gargadin cewa, duk wata jam’iyya ko dan takarar da aka samu da aikata magudin zabe za a yi masa hukunci mai tsauri.