Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya mikawa shugaban jam’iyyar APC mai mulki, Abdullahi Ganduje tayin nadin jakadanci a daya daga cikin kasashen Afirka, in ji jaridar DAILY NIGERIAN.
An nada Ganduje ne a matsayin shugaban jam’iyya mai mulki na kasa a ranar 3 ga watan Agusta, 2023, biyo bayan murabus din da Abdullahi Adamu ya yi.
- Kasar Sin Ta Kafa Cikakken Tsarin Samar Da Sabbin Makamashi Mafi Girma A Duniya
- AU Ta Naɗa Pantami Shugaban Tsara Manufofin Masana’antun Afrika Karo Na 4
Majiya mai tushe wacce ta nemi a sakaya sunanta, ta tabbatar da cewa, Tinubu ne ya turo Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio don tsakurawa Ganduje wannan mummunan batun.
A cewar majiyar, Akpabio ya shaida wa Ganduje wannan shirin ne da nufin tseratar da shi daga shari’ar zargin cin hanci da rashawa da yake fuskanta a Kano a halin yanzu.
Sai dai majiyar ta ce, Ganduje bai yi farin ciki da wannan tayin na shugaban kasa ba, inda ya ce, tuhume-tuhumen “nau’i ne na karya” kuma zai yi nasara a shari’arsa a kotu.