Batun yawan makudan kudaden da ‘yan majalisar tarayya ke karba na ci gaba da tayar da kura a Nijeriya bisa yadda aka samu bayanai masu cin karo da juna a tsakanin Hukumar Rabon Albashi ta Kasa (RMAFC) da kuma wani Sanata mai ci daga Jihar Kano, Abdurrahman Kawu Sumaila.
Ita dai hukumar, ta bayyana cewa kowane dan majalisar dattawa yana amsar albashi da alawus a kowani kimanin Naira 1,063,860, yayin da shi kuma Sanatan ya bayyana cewa Naira miliyan 21 ake biyan su a matsayin kudin gudanarwa.
- Shirin 3MTT Zai Samar Wa Matasa Miliyan Uku Aikin Yi, inji Ministan Yaɗa Labarai
- Mutum 3 Sun Rasa Rayukansu Yayin Da Ambaliyar Ruwa Ta Mamaye Ƙauyuka A Bauchi
Hukumar ta ce daga cikin dunkulallen albashin da ake biyansu da alawus, akwai tsurar albashin Naira 168,866:70, sai alawus din mai da kula da motocin naira 126,650 da naira 42,216:66, mataimaka da ma’aikatan gida naira 126,650:00, nishadi naira 50,660:00, kayayyakin aiki naira 50,660, kudin sayen jaridu naira 25,330:00, alawus din tufafi naira 42,216,66:00, kula da gida naira 8,443.33 da kuma alawus na mazabu naira 422,166:66.
Shugaban RMAFC, Muhammed Bello Shehu ne ya bayyana hakan a ranar Talata a martanin da yake mayarwa kan cece-kucen da ake yi dangane da ainihin albashi da alawus-alawus da ake biyan ‘yan majalisar dokokin tarayyar Nijeriya.
Sai dai shugaban hukumar wanda doka ta ba ta ikon daidaita albashi da alawus-alawus na masu rike da mukaman siyasa, ya ce wasu alawus-alawus ne na yau da kullum ne, yayin da wasu kuma ba na yau da kullum ba ne. A cewarsa, ana biyan alawus-alawus na yau da kullum tare da albashi, yayin da ake biyan alawus na musamman daban. Misali, akwai alawus na kayan daki naira miliyan 6,079,200 da garaturi da ake biya sau daya a kowane wa’adin mulki, sai kuma alawus din motoci na naira miliyan 8,105,600, wanda shi rance ne da za a biya bayan dan majalisa ya bar ofishi.
“Idan aka yi la’akari da albashin sanatoci na wata-wata, za a ga cewa kowane sanata na karbar albashi da alawus-alawus na naira 1,063,860:00 a duk wata, wanda ya kunshi gundarin albashi nai naira 168,866:70 da kudin man motoci na naira 126, 650:00 da kudin mataimaka na naira 42,216:66 da ma’aikata nai naira 216,66:00 da kula da gida naira 8,443.33:00 da kuma alawus na mazabu na naira 422,166:66,” kamar yadda Shugaban RMAFC ya bayyana a wata sanarwa da ya sanya wa hannu a ranar Talata.
Ya kuma jaddada cewa in ban da wasu tsirarun masu rike da mukaman siyasa da na gwamnati irinsu shugaban kasa, mataimakin shugaban kasa, shugaban majalisar dattawa, shugaban majalisar wakilai da sauran su, duk jami’an gwamnati da na majalisa ba a ba su gidaje kamar yadda aka saba a lokutan baya.
“Hukumar kuma tana son yin amfani da wannan dama wajen bayyana cewa duk wani zargi da ake yi game da wasu alawus-alawus da masu rike da mukamin siyasa, ko ma’aikacin gwamnati ke dauka a wajen da aka tanadar a cikin dokar albashi ta shekarar 2008, ya kamata a yi bayaninsa daga wanda ya yi zargin.
“Don kauce wa yada bayanan da ba su dace ba da kuma bata suna da ake yaudarar ‘yan kasa da sauran mutanen duniya, hukumar ta ga ya fi dacewa ta sanar wa ‘yan Nijeriya da duk wani mai sha’awar samun cikakkun bayanai da suka kunshi albashin masu rike da mukaman siyasa, da jami’an gwamnati, ya garzaya adireshin intanet na hukumar: www.rmafc.gob.ng, zai ga komai dalla-dalla” in ji shi.
Haka nan ya kara da cewa, tsarin mulkin kasa bai wa Hukumar RMAFC ikon tilasta aiki da abin da ta tsara a matsayin albashi ba, inda ya ce majalisar dokoki ta kasa ce ke da hurumin yin hakan.
Sai dai kuma, Sanata Kawu Sumaila na jam’iyyar hamayya ta NNPP ya ce kudaden gudanarwar da yake samu a matsayinsa na dan majalisar dattawa da ya kunshi har da tafiyar da ofishinsa ya kai naira miliyan 21 a kowane wata.
Kawu Sumaila wanda ya ce miliyoyin ba wasu kudade ba ne masu yawa da ‘yan majalisar ke samu da har za su zama wani abin cece-kuce, ya bayyana hakan ne ga BBC Hausa, bayan shugaban hukumar ta rabon albashi ya yi wadancan bayanan na sama.
“Kudin da ake karba na albashi a wata bai kai naira miliyan daya ba, idan an yi yanke-yanke yakan dawo kamar naira dubu dari shida da dan wani abu a matsayin albashi,” in ji sanatan.
Ya ce hukumar tattara kudaden shiga da raba su ta Nijeriya ce ta yanka wa ‘yan majalisar albashin.
“Saboda kari da aka samu, a majalisar dattawa ana ba wa kowane sanata naira miliyan ashirin da daya a kowane wata a matsayin kudin gudanar da ofishinsa,” in ji shi.
Ya kara da cewa jimillar naira miliyan 22 yake samu a matsayinsa na sanata.
Ya ce kudaden da yake karba su ne na dukkanin ayyukan da zai yi da suka hada da tafiye-tafiyen dan majalisa na cikin gida da sayen jaridu.
Ya ce bai san adadin kudin da shugabannin majalisar ke karba ba a matsayin albashi da na gudanarwa.
Sanatan ya caccaki Obasanjo, inda ya ce a zamanin mulkinsa ne aka fara ba ‘yan majalisa kudaden da suke wuce hankalin mutane da nufin gyara ga kundin tsarin mulki domin sahale masa yin tazarce, zargin da a baya tsohon shugaban ya musanta.
Idan za a tuna, a kwanakin baya ne tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo ya yi zargin cewa ‘yan majalisar tarayya suna biyan kansu albashi da alawus-alawus na wata-wata wanda ya saba wa dokoki. Haka kuma, tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani, ya taba bayyana cewa kowane sanata na karbar kudin gudanar da aiki a kowane wata na naira miliyan 13.5, baya ga karin naira 750,000 da hukumar ta tsara duk wata.
Wannan cacar baki na zuwa a daidai lokacin da ake fama da tsadar rayuwa a Nijeriya.
Wasu ‘yan Nijeriya na ganin makudan kudaden da ake biyan ‘yan majalisar na daga cikin dalilan da ke jefa su cikin kunci, yayin da su kuma ‘yan majalisar ke ganin nasu kawai ake gani, amma ba a dub ana bangaren zartarwa.