A yayin da zaben gwamnan Jihar Edo ke kara gabatowa, hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), ta bayyana laifukan zabe a matsayin daya daga cikin manyan barazana ga samun sahihan zabuka a Nijeriya.
An bayyana cewa hukumar ta lura cewa laifukan zabe na kara tayar da hankali a siyasance da haifar da tarzoma a cikin kasar nan.
- Kotu Ta Umarci INEC Ta Tuhumi Gwamnoni Kan Rikice-rikicen Zaben 2023
- Tinubu Ya Amince Da Karin Albashi Da Kashi 300 Ga Alkalan Nijeriya
Shugabar sashen shari’a na ofishin hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) reshen Jihar Edo, Mrs Rita Amadi ta bayyana hakan a wata takarda da ta gabatar a wani taron yini daya da kungiyoyin matasa a Jihar Edo kan rawar da matasa za su taka gabanin zaben gwamna a ranar 21 ga Satumba, 2024.
Amadi, wacce jami’in shari’a a ofishin Benin, Misis Oba Agbonifo ta wakilta, a takardarta mai suna, ‘Laifukan zabe da hukunce-hukuncensa’, ta ce makasudin gabatar da taron shi ne, a wayar da kan jama’a, musamman matasa game da dokokin zabe da kuma hukuncin da doka ta tanada ga duk wanda ya karya dokokin zabe.
Ta yi nuni da cewa gurfanar da wadanda suka aikata laifukan zabe a Nijeriya ya zama babban aiki. A cewarta, daya daga cikin manya-manyan matsalolin da ke hana gudanar da sahihin shari’a kan laifukan zabe shi ne, rashin ingancin binciken laifuka a Nijeriya.
Amadi ta bayyana cewa kokarin rage laifukan zabe zai iya yin tasiri ne kawai ta hanyar kamawa, gurfanar da masu laifi da kuma hukuntasu, domin nuna izina ga masu sha’awar aikata laifi.
“Mutum ko gungun mutane na iya aikata laifukan zabe, kuma ya kamata irin wadannan mutane su fuskanci hukunci daidai da dokokin zabe da kasa ta tanada.
“Dokokinmu sun tanadi hukunci ga wadanda suka aikata laifukan zabe. Bugu da kari, matasa sun fi yawa a cikin al’ummarmu, sannan sun fi yawa ga mutanen da ke shiga harkar zabenmu a matakai daban-daban.
“A kan wannan yanayin yana da matukar muhimmanci matasa su fahimci laifukan zaben,” in ji ta.
Jami’ar shari’a ta INEC ta ce shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana hakan a wata ganawa da manema labarai, inda ya ce duk da cewa hukumar zabe ta ba ta ikon hukunta wadanda suka aikata laifukan zabe tare da rashin ikon da za su bayar wajen kamawa da kuma binciki laifukan zabe “.