Hukumar kula da raya kasa da aiwatar da gyare-gyare a cikin gida ta kasar Sin NDRC, wadda ke zaman hukumar koli mai tsara harkokin raya tattalin arzikin kasar, ta zayyana wasu muhimman ayyukan kare muhalli a kasar.
Zhao Chenxin, mataimakin shugaban hukumar, ya bayyana jiya Alhamis, yayin wani taron albarkacin ranar kare muhalli ta kasar Sin da aka yi a birnin Sanming dake lardin Fujian na kudu maso gabashin kasar Sin cewa, hukumar NDRC za ta inganta gyare-gyare a fannin kare muhalli da rage hayakin Carbon da samar da ci gaba mai inganci a kasar.
- Sin Ta Yi Kira Ga Gamayyar Kasa Da Kasa Da Su Mutunta ’Yancin Kan Sudan Ta Kudu A Lokacin Mulkin Rikon Kwarya
- Kwazon Kasar Sin A Ayyukan Shiga Tsakani Na Samun Yabo Daga Sassan Kasa Da Kasa
Hukumar za ta aiki tukuru kuma yadda ya kamata, don ganin an kai matsayin koli wajen fitar da hayakin Carbon zuwa shekarar 2030, sannan zuwa 2060, a samu daidaito tsakanin fitar hayakin da abubuwan dake iya zuke. Kana hukumar za ta inganta kokarinta na kare muhalli da karfafa hadin gwiwa da kasa da kasa wajen raya muhalli da rage fitar da hayakin Carbon.
Ya kara da cewa, NDRC za ta aiwatar da dabarun kudi da na haraji da zuba jari da batutuwan da suka shafi kayyade farashi, domin tallafawa ayyukan raya muhalli da rage fitar da hayakin Carbon.
Haka kuma, hukumar za ta zurfafa hadin gwiwa da kasashen duniya ta fuskar tattalin arzikin bola jari da yayata ingantattun fasahohi da kayayyaki da mizanin inganci da dabarun kasuwanci domin inganta rage fitar da hayakin Carbon, tare da shiga ana damawa da ita a harkokin da suka shafi yanayi a duniya.
A bara, majalisar wakilan jama’ar kasar Sin ta kada kuri’ar ayyana ranar 15 ga watan Augusta a matsayin ranar kare muhalli ta kasar, da zummar kara wayar da kan jama’a da daukar matakan kare muhallin halittu. (Mai Fassara: Fa’iza Mustapha)