A shekarun baya bayan nan, yunkurin da kasar Sin ke yi na shiga tsakani da nufin dakile tashe-tashen hankula, da wanzar da zaman lafiya tsakanin sassan kasa da kasa na kara samun karbuwa, inda karin kasashe musamman masu tasowa ke jinjinawa salon diflomasiyyar Sin a fannin shiga tsakani da warware rikici.
An ga irin wannan kwazo na Sin a wannan gaba da rikicin Rasha da Ukraine ke shiga wani sabon mataki, inda kawo yanzu Sin din ke ta gabatar da shawarwari, da neman a kai zuciya nesa, ba tare da goyon bayan bangare guda na rikicin ba.
- Ɗan Takarar Shugaban Ƙaramar Hukuma Zai Biya Naira Miliyan 10 A Kano
- Birtaniya Za Ta Wahala Idan Likitocin Nijeriya Suka Bar Kasar – Ministan Lafiya
Salon diflomasiyyar Sin a fannin kawo karshen rikici bai sauya ba, an ga yadda a watannin baya kasar ta shiga tsakanin kasashen Saudiyya da Iran, har aka kai ga sassauta halin rashin jituwa dake tsakaninsu.
Kaza lika, an ga irin yadda Sin din ke ta gabatar da shawarwari, da goyon bayan shiga tsakani a rikicin Isra’ila da Falasdinawa, da yadda ya kai ga wanzar da zaman lafiya da lumana a daukacin shiyyar gabas ta tsakiya.
Har kullum, burin Sin shi ne ganin duniya ta kasance cikin yanayi na lumana, da dakatar da fito na fito a sassan dake fuskantar rikici. Bisa wannan manufa ne ma a baya bayan nan wakilin musamman na gwamnatin Sin game da harkokin Turai da Asiya Li Hui, ya ziyarci kasashen Brazil, da Afirka ta kudu da Indonesia, a matsayin matakin jan hankali, da neman goyon baya ga manufar Sin ta tabbatar da kwantar da kura, da kawo karshen tashe-tashen hankula.
Bisa wannan muhimmin kokari, kasashen da Li Hui ya ziyarta, da ma sauran kasashen duniya masu goyon bayan zaman lafiya, sun jinjinawa kwazon Sin, suna masu fatan yin aiki tukuru tare da kasar domin kaiwa ga nasarar da ake fata.
Karkashin manufar Sin ta cimma nasarar samun cikakken zaman lafiya a duniya, Sin ba ta taba rura wutar tashin hankali ba, ko kokarin cin gajiya daga yaki. Maimakon hakan, tana tsaya wa gaskiya da adalci, da mara baya ga neman cimma matsaya tare da sassan kasa da kasa, don tabbatar da ganin duniya ta koma kan turbar zaman lafiya da lumana, ba tare da mayar da wani bangare “Saniyar ware ba”!