A jiya Juma’a, kasashen Sin, da Laos, da Myanmar, da Thailand sun gudanar da kwarya-kwaryar taron ministocin harkokin waje, a birnin Chiang Mai na kasar Thailand. Inda ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya bayyana cewa, har yanzu halin da ake ciki a kasar Myanmar yana sanya mutanen duniya damuwa. Sai dai a ko da yaushe, kasar Sin na bin ka’idar rashin tsoma baki cikin harkokin gida na sauran kasashe, kana tana goyon bayan kasar Myanmar, wajen cimma sulhu a cikin gida ta hanyar yin shawarwari tsakanin bangarorin kasar daban daban.
Bugu da kari, kasashe hudu da suka halarci taron sun amince gaba daya, da a kara kokarin yaki da laifukan da suka shafi kan iyakokin su, kamar caca ta yanar gizo, da damfara ta hanyar sabbin fasahohin sadarwa, da safarar miyagun kwayoyi, da fataucin mutane, tare da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankinsu baki daya.
Kaza lika a Juma’an, yayin da yake jagorantar taron ministocin harkokin waje na kasashen dake dab da kogunan Lancang da Mekong karo na tara, Wang Yi ya gabatar da shawarwari guda hudu, game da hadin gwiwa tsakanin kasashen, inda ya ce ya kamata a kare zaman lafiya da kwanciyar hankali, da sa kaimi ga bunkasuwar kirkire-kirkire, da neman ci gaban tattalin arziki bisa hadin gwiwarsu, da inganta mu’ammala tsakanin al’ummun kasashen. (Bello Wang)