Ƙungiyar tsofaffin ma’aikata ta Nijeriyar (NUP) ta bayyana cewa wasu d suka yi ritaya na karɓar ƙananan kuɗaɗe kamar Naira ₦500 a matsayin fansho a wata.
Alhassan Musa, Sakataren NUP na Jihar Kaduna, ya bayyana cewa halin da ya sa waɗannan tsofaffin ma’aikatan ke cikin mawuyacin hali, musamman a kudancin ƙasar nan da jihohin da ke samar da mai duk da cewar suna samun kuɗaɗen tallafi masu yawa daga Gwamnatin Tarayya.
- Dokar Fansho Ta Majalisar Dokoki: Dokar Son Kai Ko …?Kanun Labarai
- Gwamnan Zamfara Ya Biya ‘Yan Fansho Hakkokinsu Fiye Da Nb7
Ya ce har gwamma wasu jihohin Arewacin ƙasar da Abuja, inda fansho ke tsakanin Naira 3,500 zuwa Naira 18,000, sai dai a Jihar Kaduna mafi ƙarancin fansho Naira 30,000 a shekarar 2020 a zamanin mulkin Gwamna Nasir El-Rufa’i.
Musa ya yi kira da a sake duba ƙarin kashi 50% a mafi ƙarancin fansho duba da yanayin tattalin arzikin ƙasar a halin yanzu.
Ya jaddada cewa NUP ta yi wannan kira ne tun lokacin da mafi ƙarancin albashi na ƙasa ya kasance Naira 30,000, kuma tana tsammanin da sabon albashin Naira 70,000, tsofaffin ma’aikata su ma za su samu irin wannan ƙarin.
Ya kuma ce bai kamata wani tsohon ma’aikaci ya rika karɓar ƙasa da Naira 70,000 ba, yana mai yin kira da a tabbatar da adalci tsakanin kuɗaɗen da ma’aikata masu aiki da tsofaffin ma’aikata ke samu.