Sarkin makafin Katsina, Alhaji Garba Muhammad Mahuta ya bukaci wadanda yake shugabanta da su mallaki katin zabe kafin wa’adin ranar 31 ga watan Yuli ya cika.
Alhaji Garba ya yi kiran ne a zantawar da ya yi da manema labarai a Jihar Katsina.
Ya yaba wa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) game da ware ranaku biyu saboda mutane masu bukata ta musamman su mallaki katin zaben.
Alhaji Garba ya ce da katin zaben ne kadai mutane za su iya zabar wa kansu shugaban da ya kwanta masu a rai.
Mutanen da shekarunsu suka kai jefa kuri’a na ci gaba da yin tururuwa zuwa ofisoshin INEC da ke karamar hukumar Mani da Mashi don su mallaki katin zaben kafin wa’adin yin rajistar ya cika.
Sarkin makafin Katsina wanda ya nuna damuwarsa game da hare-haren ‘yan ta’adda da yin garkuwa da mutane. Ya yi kira ga al’ummar musulmi da su dukufa wajen yin addu’o’i da gudanar da azumi domin neman agajin a kan matsalolin da suka addabe su.
Alhaji Garba wanda kuma shi ne sakataren kungiyar nakasassu ta kasa, inda ya yi kira ga mutane masu hannu da shuni da kungiyoyin ba da agaji da su taimaki ma-su karamin karfi domin su samu sa’ida daga tsadar rayuwa da ake fama da ita a halin yanzu.