Akalla mutane 12 ne suka mutu a garin Daki Takwas da ke karamar hukumar Anka a Jihar Zamfara, bayan shan miyar ganyen lalo mai dauke da maganin kashe kwari.
Mutane 25 ne da suka fito daga gidaje biyu suka sha miyar a ranar Juma’a, inda tun a lokacin suka fara rasuwa.
- Shugaban Ƙasa Tinubu Zai Sake Ficewa Zuwa Faransa
- Jami’an Sin Da Rasha Za Su Jagoranci Taron Karo Na 28 Na Kwamitin Kula Da Tattaunawa Tsakanin Firaministocin Sin Da Rasha
Yanzu haka dai akwai mutane tara daga cikinsu da ke kwance a asibiti.
Daraktan Kula da Lafiyar Al’umma kuma jami’i mai Kula da cututtuka masu yaÉ—uwa a jihar, Dakta Yusuf Abubakar Haske, ya bayyana yadda al’amarin ya faru.
Ya tabbatar da cewa shan miyar da aka yi da ganyen lalon ce ta yi sanadiyar mutuwar mutanen.
“Manomi ne ya je ya yi feshin kwari a kan abin da ba ya so, daga ciki akwai wani ganye da ake kira lalo, wanda ana miya da shi a gidajenmu na Hausawa. Su kuma mutanen ba su san ya yi ba.
“Ya yi feshin da safe, su kuma suka je da rana domin nemo ganyen da za su yi miya. Daga bisani sai suka kamu da amai da gudawa da zubar da yawu. Daga nan ne aka dauke su zuwa asibiti, domin a ba su taimakon gaggawa.
Ya ce kasancewar wasu sun fi wasu shan miyar, sai ya kasance wasu sun mutu a gida yayin da wasu kuma a wani asibiti a Anka suka mutu.
Wasu kuma sai da aka kai su Babban Asibitin Tarayyar jihar sannan suka rasu.
Amma ya ce jihar ta shirya don tunkarar lamarin.