Cibiyar bunkasa zuba jari a nahiyar Afrika ta kasar Sin (CABC), ta kaddamar da rahoto kan jarin da kamfanonin kasar Sin suka zuba a nahiyar Afrika na 2024.
Rahoton wanda aka kaddamar da yammacin jiya Juma’a, ya bayyana nasarorin da aka samu da sabbin bangarori da ma damarmakin zuba jari dake akwai a kasashen Afrika.
- Kasar Sin Ta Kara Ware Kudaden Agajin Gaggawa Ga Lardin Liaoning Dake Arewa Maso Gabashin Kasar
- Kasar Sin Ta Harba Sabon Tauraron Dan Adam Na Sadarwa
A kan fitar da rahoton a kowacce shekara tun daga shekarar 2021. Wannan sakamako ne na dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afrika FOCAC, karkashin jadawalin aikin da ake son gudanarwa daga 2021-2024, wanda aka fitar a Dakar na kasar Senegal. Kuma a bana, rahoton na zuwa ne gabanin taron na FOCAC wanda za a yi a Beijing, daga ranar 4 zuwa 6 ga watan Satumba mai zuwa.
A jawabinsa na bude taron, babban shugaban majalisar CABC, Wang Xiaoyong ya bayyana dandalin FOCAC a matsayin wata kadara mai daraja ga Sin da Afirka.
Yana mai cewa, sun yi ammana cikin shekaru 3 masu zuwa, karkashin dabaru daga gwamnatocin Sin da Afirka, da goyon baya daga bangarorin diplomasiyya da cinikayya da hada-hadar kudi, hadin gwiwar Sin da Afrika a bangarorin tattalin arziki da cinikayya da zuba jari, zai kai ga zamanantar da nahiyar Afrika.
A cewar rahoton, zuwa karshen shekarar 2022, jarin da Sin ta zuba kai tsaye a nahiyar Afrika ya zarce dala biliyan 47, kuma sama da kamfanonin Sin 3,000 ne suka zuba jari tare da gudanar da harkokin kasuwanci a Afrika. kana a rabin farko na shekarar 2023, jarin kai tsaye na Sin a Afrika ya zarce dala biliyan 1.82, wanda ya karu da kaso 4.4 a kowacce shekara.
Rahoton ya kara da cewa, kasar Sin na kara yawan jarinta a Afrika a bangarori daban daban, inda ta kara fadadawa zuwa bangarorin masu tasowa kamar na tattalin arzikin dijital da ayyukan masu kare muhalli da sufurin sama da hidimomin kudi da cinikayya ta yanar gizo da sauransu.
Bugu da kari, rahoton ya ce ta hanyar zuba jari dake mayar da hankali ga harkokin kasuwanci, jarin Sin kan ababen more rayuwa da sauran sabbin bangarori suna bunkasa tsarin ayyukan masana’atu da ma daukaka darajarsu.
Da yake jawabi, tsohon ministan kudi da tsare-tsare na kasar Habasha kuma mai neman digirin-digirgir a cibiyar nazarin hadin gwiwar kasashe masu tasowa a jami’ar Peking ta kasar Sin Endalkachew Sime, ya bayyana rahoton a matsayin mai muhimmanci wajen tsara dabaru da manufofi, saboda yadda ya yi bayani dalla-dalla kan bangarorin hadin gwiwa da wadanda ya kamata a mayar da hankali kan su, da ma kalubalen da ake fuskanta. Haka kuma zai kara aminci tsakanin bangarorin biyu da kyautata muhallin hadin gwiwa.
Shi kuwa masanin tattalin arziki kuma tsohon ma’aikacin bankin duniya kuma mashawarcin shugaban kasar Kenya kan harkokin tattalin arziki, Dr. Mwangi Wachira, cewa ya yi, yayin da kasashen nahiyar Afrika ke kokarin neman ci gaba, kasar Sin ta tallafawa wannan kokari ta hanyar gudanar da ayyukan da suka taimaka wajen magance tushen manyan kalubalen nahiyar.
Ya ce ana samun nasarar hadin gwiwar bangarorin biyu ne saboda manufofin Sin a bayyane suke, kuma tana taimakawa ba tare da kakaba akidunta kan su ba, wato tana taimakawa wajen zamanantar da Afrika, ta hanyar da ta dace da Afrika.
Rahoton ya ce za a kara karfafawa kamfanonin Sin gwiwar zubawa da fada jarinsu a kasashen Afrika, tare da kira ga gwamnatocin nahiyar Afrika su kyautata muhallin kasuwanci da inganta dangantakar Sin da Afrika. (Fa’iza Mustapha)