Shafin Taskira shafi ne daya saba zakulo muku batutuwa daban-daban wadanda suka shafi al’umma, ciki sun hadar da zamantakewar aure, rayuwar yau da kullum, rayuwar matasa, soyayya da dai sauransu. Tsokacin mu na yau zai yi duba ne game da batun da wasu matan ke yi na ganin cewa auren mijin wata wayewa ne, yayin da wasu ke ganin hakan ba wayewa bane rashin dacewa ne.
Wannan dalili ya sa shafin Taskira jin ta bakin wasu daga cikin mabiyansa game da wannan batu; Ko mene ra’ayinsu game da hakan? Wane irin amfani ko rashin amfani auren mijin wata ke da shi?, Wace shawara za a bawa mata masu auren mijin wata dan wata manufa ko bukata?.
Ga dai ra’ayoyin nasu kamar haka:
Sunana Hassana Yahaya Iyayi (Maman Noor), Jihar Kano:
Babbar magana wai an ce da makasa’u bawa Wallahi babu wata burgewa ga auren mijin wata Hajiya, ki auri saurayi ku barje soyayya da dumi-dumi ya fi, atoh Hmmm.. wallahi babu wata wayewa sai dai rashin babu wani sai a fake da wayewa. Ra’ayina gaskiya shi ne gwara dai su auri samari ya fi sauki in kuma babu saurayin sai a yi maleji da mijin wata a fake da wayewa. To sai mu ce aji tsoron Allah a shigo da farar aniya, idan kin shigo dan ki kori wata koma dai wani abun na daban haka zalika za a yi miki wata ita ma! ta ce Allan bur in ba shi ba sai rijiya, kina ji kina gani ke ma ki fice wata tayi wuf da shi aji tsoro Allah dai ‘yan mata da zawarawa masu shiga gidan wata ko kwace miji wata dan wata bukata ta kai to.
Sunana Hafsat Sa’eed Daga Neja:
Hm.. Ni wannan abun ma ya daure min kai, ai namiji mijin mace hudu ne ba wai da mace daya kawai aka yi shi ba, koda ace ba wayewa bace amma addini ne wanda Allah subhanahu wata’Ala ya hukunta namiji ya auri mace hudu, ni a ganina hakan ba wani matsala ba ce, indai an daidaita shikkenan ko mace na so ko ba ta so sai an yi, amma batun wayewa ce ko ba wayewaba ce bana ce ba.
Sunana Rabi’atu Bashir Abdullahi (Ummu Maher Miss Green), Jihar Kano:
Gaskiya ni a ganina wayewa ne, saboda sai an kai kudi kasuwa ake sanin darajarsu, idan da baki shiga gidan wata ba to ba lallai ne ki san rayuwa ba, amma shigarki cikin gidan shi zai sa ki nuna kin isa mace. Amfaninsa shi ne sanin ilimin duniya, da kuma kara wayewa da wadansu abubuwan. Gaskiya shawarar da zan bawa mata, su ji tsoron Allah idan kin shiga domin cutar da wata to, fa kanki ki ka cuta. kuma duk abin da kayi sai an yi maka.
Sunana Aisha isah Abubakar Gama Mai Waka (Aisha Gama) Jihar Kano Gama:
Tabbas! akwai matan da suke auren mijin wata da wata manufa wanda su suka bar ma kansu sanin dalilai da dama mafi yawa kwadayin abin duniya ne yake kai hankalin su gidan, wasu kuma burunsu su fidda ta cikin gidan, wasu ma cin amana ne sabida su hana ta cikin gidan kwanciyar hankali, idan taki hakuri kuma shikkenan ta samu abin da take so burinta ya cika to koma me ya kawota ke ta cikin gidan ina me jan hankalinki da ki yi hakuri, wallahi koda me ta zo gidan nan idan da alkairi ta zo ko akasin haka ki yi hakuri wallahi Allah ba zai bari ta cutar dake ba kina zaune Allah zai duba lamarin kuma zai shiga lamarin in sha Allah. Shawara ga masu shiga gidan mijin wata da wata manufa wallahi ku ji tsoron Allah duk da abin da ki ka shiga Allah ya fi mu sani kuma duk da nufin da ki ka shiga Allah yana ganinki shi hakkin aure ba sai an je lahira ba wallahi tun daga duniya Allah yake fara sakayya, sabida haka ta gida ki yi hakuri Allah yana tare dake in sha Allah.
Sunana Firdausi Kano, Daga Jihar Kano:
A ra’ayi na dagewa akan auren mijin wata rashin wayewa ce da rashin sanin darajar kai, a wannan zamanin da muke ciki da saurayi da mai Mata duk kowanne da matsalar sa, abin da ya kamata mata su gane shi ne aure bauta ce ta ubangiji kuma aljanna muka je nema ba wani abin ba. Mafi yawan matan da suke dagewa sai sun auri mijin wata tashin hankali ne yake kai su kuma tun daga waje kasan ba za su yi zaman lafiya da uwargida ba. Ni a wajena auran mijin wata ba shi da amfani saboda in ke ce za a yi wa kishiya ba za ki ji dadi ba. Shawarar da zan ba su shi ne su ji tsoron Allah kar su manta da hadisin da yake magana akan ka so wa dan’uwanka abin da ka so wa kanka, Kuma su yi addu’ar zabin ubangiji a rayuwar su.
Sunana Fatima Tanimu Ingawa Jihar Katsina:
A ganina masu ganin auren mijin wata wayewa ne, kila a nata bangaren tana da dalilin ta hakan kuma masu ganin ba wayewar bane suma da nasu dalilin. Ga yara ‘yanmata masu ganin cewar auren mijin wata wayewa ce, ina ganin wannan aiki ne na yarinta don kallon kitse suke wa rogo. Hujjar su da dama ba ta wuce irin zamantakewar da suke hasasowa a gidanjen mijin wasun, wanda gimshinkin zamantakewar basu san da wani irin tubali matan suka dasa shi ba. Gara ma ga bazawara da ta san ciwon kanta, ta san wanenen ya dace da zabin ta. Auren mijin wata dadinsa daya, in Allah ya sa an yi dace da matar ta sa ta farko ta dora sa a kan tarbiyya mai kyau, abun da ya sa na kira hakan da tarbiyya kuwa shi ne; abubuwan da ta sabar masa ta kuma gogar da shi akai. Misal; kyautatawa a ciyarwar abinci mai kyau, tufatarwa, kyauta, mutunta dangi da dai sauraransu. In akai rashin sa’a ta sabar mai da mako da karanta, da kuma rashin sakar masu yadda ya dace sai kuma a samu matsala. Domin duk wacce ta shigo akan wannan takidin za ta dasa. Shi ya sa a wani bangaren ka kafa gidanka da kanka ya fi (ma’ana kai ‘starting home’ dinka). Shawara ta akan masu auren mijin wata da wata manufa ya kamata su daina, domin da dama manufar ba ta alkhairi ba ce saboda niyyar, sau da dama nasu anshe gidan ne, ko a ma fidda uwargidan da aka samu. In Allah ya kaddare mace da auren mijin wata to ta kyautata niyar ta, ta kuma shiga da niyar ibada, ta kuma mutunta wadda ta taras. Biyayya, kyautatawa, addu’a da da’a sune dai muhimman ginshikai na kowanne zamantakewa.
Sunana Yareema Shaheed, Jihar Kano:
Auren mijin wata wayewa ne tare da wayau da kuma sakacin wasu matan, domin duk wanda ta zo ta aure miki miji to ke ce ki ka ba da kofar yin haka tun farko wajen zayyana ma kawar taki sirrin da ke tsakaninki da mijinki. Amfanin auren mijin wata zai sa ita uwar gidan ta kara sanin rayuwa tare da yin taka-tsam-tsam. Mata masu auren mijin wata ba su da wata matsala, domin ita uwar gidan ce ta ba da damar yin haka, don haka ta ci gaba da rikon sabon angonta.
Sunana Aminu Adamu Malam Madori A Jihar Jigawa:
To magana ta gaskiya shi dai aure ibada ne, kuma muddun an bi matakan da suka dace wajen neman auren ai babu wata matsala don mace ta auri mijin wata ko kuma ace mai mata tunda dama addini yayi umarni a auri sama da daya muddun mutum yana da halin rike su kuma yana da yakinin zai yi adalci a tsakaninsu ba nuna bambanci ko fifiko ba. To magana ta gaskiya auren mutum mai aure ma a lokuta da dama ya fi, domin muddun mutumin yana da halin rike matan ya fi bada kulawa da kiyaye hakkin aure ta kowace fuska sabanin saurayi ko mara mata, don haka za ka gani wasu ‘yan matan da dama sun fi so mai mace ya zo neman aurensu domin sun san za su samu kulawar da ta dace a wajen fiye da saurayi ko mara mata. To shawara a nan ita ce ya kamata da farko ma ake kallon auren a matsayin ibada ta haka ne za a ke kiyaye dokokinsa, sannan kuma za a bi hanyar da ta dace wajen neman auren ko saurayi ko kuma ma mai mata, domin sanin ilimin zamantakewar auren shi ne abun da ya fi komai muhimmanci kuma shi ne abun da zai taimaka wajen auren yayi karko, kuma ake mutunta juna a zamantakewar auren, daga karshe nake addu’ar Allah ya kawo mana karshen wannan matsala ta tsadar rayuwa dama tsananin talauci daya jawo ake samun yawaitar mace-macen aure musamman a kasar Hausa.
Sunana Muhammad Isah Zareku Miga, Jigawa:
Akan batun auren mijin wata na farko dai addinin Musulunci ne ya tanaji yin hakan mutukar za ka iya yin adalci. Amfanin aure mijin wata shi ne mace za ta kasance ita ma da aurenta mai makon ta zauna haka a matsayin budurwa ko bazawara. Rashin amfani kuma shi ne mace za ta zama ba ta da aure sai ta zo tana jiran wani. A maimakon ta auri mijin wata don ta rufawa kanta asiri. Shawara a nan ita ce; Duk matar da take auren mijin wata don bukatar kanta ko wata manufa ya kamata ta ji tsoron Allah.Ta aure shi don ta zauna zaman aure na mutukarraba ba don wani dalili ba na karin kanta.
Sunana Anas Bin Malik Achilafia Yankwashi A Jihar Jigawa:
Da farko dai wayewa a matsayin mu na musulmai shi ne bin tafarkin sunna sau da kafa, kenan idan an fahimce ni za a lura cewa auren mijin wata abu ne mafi dacewa ƙwarai, domin yin hakan bai zama da haramci ba. Sai dai kuma ta fuskar al’ada wadda ya danganta da irin alaka dake tsakanin wacce za ta aure mata mijin. Saboda haka ni a fahimta na auren mijin wata abu ne da ya dace, domin yin hakan ma yana iya haifar da alkairai tsakanin wadda aka aure mata mijin da wacce ta aura, matukar dai sun cire son rai ko zuciya. Shawara ta dangane da wannan batu shi ne aji tsoron Allah a tsarkake niya akan komai, wanda Manzon Allah (S.A.W) ya koyar da yin hakan kafin yin komai. Idan mace ta yi haka ne domin wata manufa mummuna to fa makawa sai ta ga sakamako mummuna ko da ranta ko bayan ranta. Allah sa mu dace.
Sunana Abubakar Dahiru Abdullahi Madaci Kirikasamma A Jihar Jigawa:
Da farko dai ni ana wa ra’ayi auren mijin wata ba za a ce masa waye ba kuma ba za ace ba wayewa ba ne, kaitsaye ya danganta da dalilin da ya sa aka yi auren idan gyara ne, sannan kuma zuciya daya ne, wannan wayewa ne, idan kuma saboda abin duniya ne kudi ko da kuntatawa ita wacce take gidan to wannan ba wani abun wayewa a ciki, asali ma rashin wayewa ne ta karshe, domin a addinance aure ana yinsa ne domin Allah a matsayin ibada. Sannan anfanuwar auren mijin wata shi ne zai rike ta hannu biyu fiye da wanda baida Aure. Rashin amfanin auren mijin wata shi ne idan aka samu matsalar abokiyar zama wacce take da tashi hakali, to hakika matar za ta sha wahala, sannan ba za a samu kwanciyar hakali ba a gidan. Shawarata ga mata ku kaucewa Auren mazan wasu domin abin da suke da shi na wadata saboda in wataran an dace wataran ba za a dace ba, sannan ba haushe ya ce idan da kwadayi akwai wahala.
Sunana Lawan Isma’il (Lisary) Rano, Jihar Kano
Ra’ayina a nan shi ne wayewa ne mana, yana da amfani a nawa ganin, sabida watakila wacce ta auri mijin watan ta gano wata matsalane a gidan wadda ita ta gidan ta kasa gyarawa ita kuma ta zo domin gyara wannan matsala din. Shawarata a nan ita ce kada ki yi aure domin ki ga kin fitar da ta gidan wannan bai dace ba domin aure ibada ne duk da addininmu ya yarda ayi aure domin addini, nasaba, dukiya, da kuma kyau, to duk da haka ayi domin Allah da kuma zuciya daya kada ki yi domin uzzurawa wata matar ko shi kansa mijin. Allah ya sa mu dace amin.